Murna: Kare ya diro daga bene hawa biyu ya karya wuyan mai shi

Wani dan kasar China da yake kiwon kare a gidansa yanzu haka na jinyar karaya wuya a asibiti, bayan da karensa ya diro akan wuyansa daga benen gidan hawa biyu don murnar dawowarsa gida da kuma yi masa gaisuwa. Wanda ya mallaki karen da ake kira da sunan mahaifinsa Liu yana da shekara 67. Lamarin […]

Murna: Kare ya diro daga bene hawa biyu ya karya wuyan mai shi

Karen da ya diro daga bene gefe kuma benen ne

Wani dan kasar China da yake kiwon kare a gidansa yanzu haka na jinyar karaya wuya a asibiti, bayan da karensa ya diro akan wuyansa daga benen gidan hawa biyu don murnar dawowarsa gida da kuma yi masa gaisuwa.

Wanda ya mallaki karen da ake kira da sunan mahaifinsa Liu yana da shekara 67. Lamarin ya faru ne bayan ya dawo gidansa da ke birnin Yongzhou a Lardin Hunan na kasar China, bayan ya ziyarci ’yan uwansa. A cewar Liu, ya ce “Na yi zaton wani abu mai nauyi ya fado min a kaina ta baya daga saman ginin gidan,” hakan ya sa nan take ya sume ya fadi daga bisani ’yan uwansa suka kira motar daukar marasa lafiya aka wuce da shi asibiti.

A yayin da yake ganawa da kafar slabarai ta Sina News game da abin da ya same shi. Liu ya ce, zai iya tunawa da farkon lokacin da ya farka a asibiti ya yi tunanin ginin gidansa ne ya fado masa a ka daga bisani ya gano cewa ashe karensa ne diro a kansa daga saman benen.

A cewar Liu, ganin yadda ya yi kwanaki ba ya gidan sai karen ya taso cikin murna don yi masa barka da zuwa, hakan yasa yana hango shi ya duro tun daga saman benen sai kansa.

Liu na jinya ne a asibitin First People’s da ke babban birnin Zhangzhou, kuma binciken likitoci na bayyana cewa dirar da karen ya yi a wuyan Liu ya yi sanadiyyar karyewar kashin wuyansa. Likitocin asibitin sun ce a yanzu sai dai a yi wa Liu tiyata a kashin bayansa don daidaita karayar da ya yi.

Duk da haka Liu ya ce bai ga laifin karensa ba. Amma yana fata irin haka ba zai sake faruwa ba nan gaba. Tuni iyalan Liu suka kama karen suka  daure da igiya a wani sashe na karshen gidan.

’Yar Liu ta bayyana wa wakilin Sina News duk iyalan Liu sun firgita ganin cewa, ’yan watanni kadan da suka gabata ne aka kiwata karen amma har zai iya yin tsallen da ya kai mita shida zuwa bakwai ya diro a kan mahaifinsu.

’Yar Liu ta kara da cewa, abin mamaki duk da wannan tsallen da karen ya yi, ko rauni bai yi ba.

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas

Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS