Murnar hawa sarauta: Sarkin Saudiyya ya raba wa jama’ar kasar kyautar Naira tiriliyan shida

Sabon Sarkin Saudiyya Sarki Salman bin Abdul’aziz Al Sa’ud y araba biliyoyin Fam din Ingila ga jama’ar kasar domin murnar hawarsa kujerar sarauta. Sarki Salman bin Abdul’aziz ya bayar da kyautar da ta kai Fam biliyan 20 da miliyan 700, (kimanin Naira tiriliyan shida da biliyan 210) ne domin murnar zama Sarkin kasar.A wani sakon […]

Murnar hawa sarauta: Sarkin Saudiyya ya raba wa jama’ar kasar kyautar Naira tiriliyan shida
Murnar hawa sarauta: Sarkin Saudiyya ya raba wa jama’ar kasar kyautar Naira tiriliyan shida

Sabon Sarkin Saudiyya Sarki Salman bin Abdul’aziz Al Sa’ud y araba biliyoyin Fam din Ingila ga jama’ar kasar domin murnar hawarsa kujerar sarauta.

Sarki Salman bin Abdul’aziz ya bayar da kyautar da ta kai Fam biliyan 20 da miliyan 700, (kimanin Naira tiriliyan shida da biliyan 210) ne domin murnar zama Sarkin kasar.
A wani sakon shafin Twitter – da fiye da mutum dubu 350 suka rarraba – Sarkin ya rubuta cewa: “Jama’ata abar kauna: Kun cancanci fiye da haka, duk abin da zan yi ba zan iya ba ku abin da kuka cancanta ba.”
Kudin ya hada da kyautar albashin wata bibbiyu ga dukkan ma’aikatan kasar da sojoji da dalibai da ’yan fansho.
Tuni mutanen Saudiyya da ke cike da farin ciki suka fara sayen sababbin manyan wayoyin hannu da agoguna masu tsada tare da zuwa yawon bude ido a wurare masu tsada don murnar wannan karimci.
Wasu mazajen kuma an ce sun kebe kudin domin yin aure fari ko kara ta biyu da ta uku.
Kyautar Sarkin ta hada da kaso na musamman ga kungiyoyin kwararru da na wasanni da wasu cibiyoyi.
Daraktan rukunin kamfanonin Ashmore a yankin Gabas ta Tsakiya Mista John Sfakianakis, ya shaida wa jaridar New York Times cewa: “Yanzu haka ana dabdala a Saudiyya.”
Kyautar za ta kara gwabin albashin ma’aikatar kasar da aka kiyasta yawansu a kan mutum miliyna uku. Kuma tuni mutanen Saudiyya suka shiga nuna murnarsu inda daya daga cikinsu ya tura wani faifan bidiyo ta intanet yana ruwan Riyal a kan dansa.
An ruwaito cewa kamfanoni masu zaman kansu ma sun ba sahun Sarkin inda suka bayar da kyaututtukan albashi ga ma’aikatansu.
A watan jiya ne Sarki Salman mai shekara 79 a duniya yah au karagar mulkin kasar bayan dan uwansa Sarki Abdullah ya rasu yana da shekara 90.
Al’ada ce a Saudiyya sabon Sarki ya dadada wa jama’arsa ta hanyar yi musu kyauta a duk lokacin da ya hau karaga. Kuma wannan al’ada tana aiki inda ake samun rahotannin kamfanoni na girka manyan alluna a sassan kasar da ke cewa sun yi “Mubayi’a” ga sabon Sarkinsu.