Murnar Zaben Buhari: Matashi ya kuduri tafiya a kasa daga Ibadan zuwa Abuja
A jiya Alhamis da safe ne wani matashi mai shekaru 29 da haihuwa mai suna Sulaiman Hashimu, da ke zaune a birnin Ibadan, ya kama hanyar tafiya a kasa daga Ibadan zuwa Abuja, domin nuna farin cikinsa da nasarar lashe zaben zama sabon Shugaban kasar Najeriya da Janar Muhammadu Buhari ya yi a zaben da […]
A jiya Alhamis da safe ne wani matashi mai shekaru 29 da haihuwa mai suna Sulaiman Hashimu, da ke zaune a birnin Ibadan, ya kama hanyar tafiya a kasa daga Ibadan zuwa Abuja, domin nuna farin cikinsa da nasarar lashe zaben zama sabon Shugaban kasar Najeriya da Janar Muhammadu Buhari ya yi a zaben da aka gudanar, a ranar Asabar da ta gabata.
Matashin wanda ke aiki a karkashin kamfanin JIRADE Nigeria Limited, ya ce: “Ni dai Allah Ya sanya mani kaunar Janar Muhammadu Buhari a zuciyata, domin dukkan mutanen da muke tare da su sun yi shaidar haka. Kuma yau shekaru 2 da wucewa ke nan da na yi rantsuwa da alkawarin cewa idan Allah Ya sa Buhari ya ci zabe, to ni kuma zan yi doguwar tafiya daga ko’ina nake, in taka a kasa ba tare da na hau babur ko mota ko keke ko wata dabba ba zuwa birnin Abuja, domin gane wa idanuna ranar da za rantsar da shi a kan wannan kujera. Zan yi hakan ne domin kaunar da nake yi wa Buhari.”
Sulaiman dai dan asalin garin Funtuwa ne ta Jihar Katsina. Ya bayyana wa wakilinmu wannan nufi nasa ne da yammacin ranar Laraba, a wajen wata liyafar cin abinci da yin ban kwana da abokan zamansa, a unguwar Ojo cikin birnin Ibadan. Ya ce: “Na riga na yi wannan alkawari kuma a kulluyaumin ina rokon Allah (SWT) Ya ba ni ikon cika alkawarin da na yi. Saboda haka ga ranar cika alkawari ta zo, shi ne na yi babban tanadi domin wannan tafiya. Tanadi na farko shi ne, na tabbatar da koshin lafiyar jikina kuma ina da karfin da zan iya takawa da kafafuna daga nan Ibadan zuwa Abuja. Shi ne ya sa na tara ’yan uwa da abokan arziki, da na yi wannan alkawari a gabansu, da su taya ni da addu’o’in rokon Allah Ya kare ni kuma ya kai ni lafiya.”
Da aka tambaye shi cewa, ba ya jin tsoron ’yan fashi da makami da namun daji, sai ya kada baki ya ce: “Da farko dai, abokaina da ’yan uwa da na nemi shawararsu game da wannan tafiya tun farko, sun shawarce ni da bin hanyar da ta tashi daga Ibadan zuwa Ilorin zuwa Jebba zuwa Mokwa zuwa Bida har Abuja; domin hanya ce mai hada-hadar jama’a a kowane lokaci. Abu na biyu kuma shi ne, ina son kafa shaidu da za su yi shaidar na yi wannan tafiya ba karya nake yi ba. Zan fara neman shaida daga ’yan sanda a nan Ibadan kuma a duk gari ko kauyen da karfe 6 na yamma ta yi mani, to a nan zan tsaya in kwana a gidan Sarki ko Hakimi ko Dagaci ko Mai Unguwa ko ofishin Jam’iyar APC ko kuma ofishin ’yan sanda, domin a tabbatar da na yi wannan tafiya.”
A game da irin suturun da ya tanada kuwa sai ya ce: “A yanzu dai ba lokacin sanyi ba ne amma na tanadi riguna uku da wanduna uku da ba za su zame mani matsala a kan hanya ba da takalma guda 2 da ba za su sude a kan hanya ba, wadanda za su iya jure yin tafiyar kwanaki 15 zuwa 20 da nake kyautata zaton zan isa birnin Abuja daga yau Alhamis da na fara yin wannan tafiya ta musamman.”
Ya kara da cewa: “Wannan tafiya ce da zan yi da yardar Allah, ba domin saurin zuwa da zan takurawa kaina ba. A duk wurin da na gaji zan tsaya in huta saboda haka na yi kiyasin zan yi kwanaki 15 ko 20 daga Ibadan zuwa Abuja. Kuma zan rike wayar salulu wacce batir dinta yake daukar nauyin dadewa kafin aikinsa ya kare.”
Shin Janar Muhammadu Buhari da kake yin wannan doguwar tafiya domin murnan cin zaben da ya yi, ko ya taba saninka? Tambayar da Aminiya ta yi wa matashin ke nan da ya bayar da amsar cewa: “Ni dai na san cewa zuciyar Buhari tana tare da dukkan talakawan Najeriya amma bai taba gani na da idanunsa ba kuma bai san ni ba amma ni na san shi. kauna ce da soyayya nake yi wa wannban mutumi. Ina yin kira ga dukkan ’yan Najeriya su sani cewa batun gyara da Buhari yake cewa zai gyara al’amuran da suka lalace ba karamin aiki ba ne. Kada a yi tsammanin cewa da ya kama ragamar mulki ne za a fara ganin gyara. Ba haka al’amarin yake ba. An yi wa Najeriya babban rauni da ya kai ta ga fadawa cikin halin kunci da damuwa, wanda zai dauki tsawon lokaci kafin a iya yin maganin gyambon da ke jikin kasarmu. Amma idan aka yi hakuri aka taimaka masa da addu’o’i da goyon baya, to za a ga canji.”
Game da iyali kuwa, matashin ya ce bai riga ya yi aure ba amma iyayensa suna nan da ransu. “Mahaifina yana zaune a garin Funtuwa da ke Jihar Katsina ne, a yayin da mahaifiyata take zaune a garin Ifo cikin Jihar Osun. Kuma na yi wa mahaifiyata bayani a game da wannan tafiya da na shirya yi, wadda ba ta nuna wata damuwa ba. A maimakon haka ma ta rika yi mani addu’a ne, Allah Ya kare ni, Ya kaini lafiya, Ya dawo da ni lafiya.”