Mursi ya yi mirsisi a kotu ya ce har yanzu shi ne Shugaban Masar

  Hambararren Shugaban Masar Mohammed Mursi ya gurfana a gaban kotu tare da bayyana wa alkalin cewa har yanzu shi ne halattaccen Shugaban kasar. Shi da manyan jami’an kungiyar Ikhwanul Muslimina 14 suna fuskantar tuhumar ingizawa a kashe masu zanga-zanga a wajen fadar shugaban kasar a bara.Bayan bayanin na Mursi da kin amincewa ya sanya […]

Mursi ya yi mirsisi a kotu ya ce har yanzu shi ne Shugaban Masar

 

Hambararren Shugaban Masar Mohammed Mursi ya gurfana a gaban kotu tare da bayyana wa alkalin cewa har yanzu shi ne halattaccen Shugaban kasar. Shi da manyan jami’an kungiyar Ikhwanul Muslimina 14 suna fuskantar tuhumar ingizawa a kashe masu zanga-zanga a wajen fadar shugaban kasar a bara.
Bayan bayanin na Mursi da kin amincewa ya sanya rigar fursunoni, sai alkalin ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga Janairun badi. Kuma an tafi da Mursi zuwa kurkukun Burj al-Arab da birnin Iskandariyya.
Rahotanni na farko sun nuna za a kai shi kurkukun Tora ne da ke wajen birnin Alkahira. Kuma kafin hakan an tsare shi ne a wani boyayyen wuri na soja.
An gudanar da zanga-zanga a wajen kotun da kuma wasu wurare a Alkahira.
A ranar Litinin ne aka kai Musri wani ginin kwalejin ’yan sanda a cikin jirgi mai saukar ungulu. Yayin da sauran wadanda ake tuhuma tare da shi da suka hada da Essam el-Erian da Mohammed al-Beltagi da Ahmed Abdel Aatie sun kuma an kai su ne a motocin sulke na soja.
Lokacin da Mursi ya shiga kotun ya ki ya cire shdiyar kwat dinsa don sanya farar rigar fursunoni. Kuma wadanda ake tuhumar da suke tsare a wani keji a cikin kotun sun rika rera “haram, haram.”
Lokacin da aka nemi ya fadi sunansa tsohon Shugaban kasar ya ce, “Ni ne Dokta Mohammed Mursi, Shugaban Jamhuriyya. Ni ne halattaccen Shugaban Masar. Ba ku da ikon yin wata shari’a kan abin da ya shafi al’amuran Shugaban kasa.”
Sau biyu alkalin yana dakatar da zaman kotun kafin ya dage zaman zuwa Janairu. el-Erian ya shaida wa BBC kafin fara shari’ar cewa ana musguna wa abokan tsare shi da wani irin ruwa kuma ana yawan dukansu ta yadda wasu kan sume.