…..Muryar Talaka ba ruwanta da taron Asaba – Rabi’u Faya
Shugabannin kungiyar Muryar Talakawa a Jihohi shida da ke sashen Kudu maso Yammacin Najeriya, sun ce ba da yawunsu aka yi taron ranar Asabar a garin Asaba, hedkwatar Jihar Delta, inda aka ce al’ummomin Arewa mazauna sashen Kudu maso Yamma sun goyi bayan sake zaben Shugaba Goodluck Jonathan a zaben watan gobe ba. Sun ce: […]
Shugabannin kungiyar Muryar Talakawa a Jihohi shida da ke sashen Kudu maso Yammacin Najeriya, sun ce ba da yawunsu aka yi taron ranar Asabar a garin Asaba, hedkwatar Jihar Delta, inda aka ce al’ummomin Arewa mazauna sashen Kudu maso Yamma sun goyi bayan sake zaben Shugaba Goodluck Jonathan a zaben watan gobe ba. Sun ce: “Taron na Asaba ya yi daidai da girmama cin hanci da rashawa, ta hanyar yin amfani da kudi wajen sayen ra’ayin jama’a da Shugaba Jonathan yake yi. Babu hannunmu, kuma ba da yawunmu aka yi wannan taro da wasu mutanenmu suka gwammace su zubar da mutuncinsu domin kwadayin abin duniya ba.”
Kodineto na Muryar Talaka a sashen Kudu maso Yamma, Alhaji Rabi’u Faya, shi ne ya yi wannan bayani ga ‘yan jarida a ranar Lahadin makon jiya, jim kadan bayan kammala wani taron gaugawa da shugabannin kungiyar suka yi a birnin Ibadan.
Ya ce, “mun yi wannan taron gaugawa ne domin tattaunawa a kan wannan babbar matsala da wasu manyan mutane suke neman su yi amfani da sunanmu domin bata mana suna. ‘Yan leken asiri da muka aika zuwa wajen wannan taro na Asaba sun ba mu tabbatattun bayanai da suka nuna cewa, wasu matasa marasa aiki da mata masu zaman kansu ne suka halarci wajen taron da aka raba musu kudi daga Naira dubu uku zuwa biyar. Irin mutanen da suka halarci taron ba su da laifi, domin sun ci bilis ne, inda suka koma rera wakokin “Sai Buhari.”
Shi ma Shugaba Jonathan ya gane wa idanunsa irin yadda mutane suka rika ficewa daga wajen taron a daidai lokacin da yake karanta jawabinsa.”
Alhaji Rabi’u Faya, ya yi tambayar cewa, “mene ne ya hana yin irin wannan taro tuntuni, sai a yanzu da ake shirin yin zaben shugabannin kasa? Kuma me ya hana Shugabannin al’ummomin Hausawa da Fulani da Barebari da Nufawa da Igbira da Gwari zuwa wajen taron na Asaba?
A cewarsa, su ma shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa da dalibai da ‘yan kulob ba su halarci taron ba. Hakan ya nuna ke nan an yi taron ne domin amfani da kudi don sayen ra’ayi, wajen tabbatar da cin hanci da rashawa a Najeriya.
“Saboda haka muna yin kira da kakkausan harshe ga tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji dalhatu Attahiru Bafarawa, ya daina yin amfani da dukiyar da Allah ya ba shi wajen sayar da mutunci da hargitsa al’ummar Arewacin kasa da ke zaune a jihohin Yamma . Irin abun da yayi kenan wajen rikita al’amura a mahaifarsa ta Jihar Sakkwato wanda bai yi nasara ba.” inji Rabi’u Faya.