Muryar Talaka ta gana da ’yan Arewa a Kurmi kan zabe mai zuwa

Shugabannin Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa sun yi ganawa da ’ya’yan kungiyar da ke zaune a sassan Kudu maso Yamma inda suka tunatar da su hanyoyin da suka kamata su fuskanci ’yan siyasa a lokutan zabe mai zuwa. Sakataren Kungiyar ta Kasa, Kwamared Bishir Dauda ne ya jagoranci ganawar da aka kammala a ranar Juma’a […]

Muryar Talaka ta gana da ’yan Arewa a Kurmi kan zabe mai zuwa

Wakilan Muryar Talaka tare da Shugabannin Kasuwar Gwari ta Eleyele a Ibadan

Shugabannin Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa sun yi ganawa da ’ya’yan kungiyar da ke zaune a sassan Kudu maso Yamma inda suka tunatar da su hanyoyin da suka kamata su fuskanci ’yan siyasa a lokutan zabe mai zuwa.

Sakataren Kungiyar ta Kasa, Kwamared Bishir Dauda ne ya jagoranci ganawar da aka kammala a ranar Juma’a a Kasuwar Gwari ta Eleyele a Ibadan. “Muhimmin abin da yake tafe da mu shi ne fadakarwa ga dukan ’ya’yan kungiya da sauran jama’ar Arewa da ke zaune a wannan sashe game da babban zabe mai zuwa, ku tabbata kun girmama doka da oda domin zama lafiya, kuma kada ku kuskura ku sayar da kuri’unku ga ’yan siyasa kuma kada ku bari a yi amfani da ku a matsayin gugar yasa,.” inji Bishir Dauda.

“Ku ne kuka san irin bukatunku saboda haka muke ba ku shawara ku yi amfani da lauyanku ya rubuta irin wadannan bukatu ku mika wa duk dan siyasar da ya zo neman kuri’unku. Yin haka zai kawo karshen yawan korarku daga wuraren sana’a da mahukunta ke yi a wannan sashe,” inji shi.

Ya kawo misali da Masarautar Kano da ta sanya Sarakunan Ibo da Yarbawa a cikin hakiman da Sarkin Kano Mohammadu Sanusi ya bayar da umarnin a rika biyansu albashi. Ya ce “Amma a wannan sashe al’amarin ba haka yake ba. Sai idan kun hada kanku ne, kuma za ku iya cin irin wannan moriya.”

A jawabin wakilin Muryar Talaka a Kudu maso Yamma, Kwamared Rabi’u Faya cewa ya yi “Muna maraba da irin wadannan muhimman shawarwari da shugabannin kungiya ta kasa suka sanya mu a kai kuma muna tabbatar da cewa, sakon zai isa ga jama’a. Kuma za mu nuna musu muhimmancin zaben mutanen kwarai da za su kare mutuncinmu.”

Mai masaukin baki, Shugaban Kasuwar, Alhaji Dauda Shehu ya yi magana ne a kan ’yancin dan Adam inda ya ce “A shirye muke mu sanya hannu wajen karbar dukan ’yan siyasa da suka san mutuncinmu domin samun zama lafiya da ci gaban harkokinmu a wannan kasuwa da Jihar Oyo baki daya. Ba za mu amince da wadanda suke shigowa cikinmu domin raba kawunanmu ba. Kuma za mu yi kokarin dinke barakarmu.”