Musa Wada ya zama dan takarar Gwamnan Kogi a PDP

Injiniya Musa Wada, ya zama dan takarar Gwamnan Kogi a jam’iyyar PDP, a babban zaben Gwamnan jihar da za a yi ranar 16 ga Nuwamba 2019. Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na masu neman takarar tsayawa a PDP zaben, Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ne ya sanar da hakan a yau. Gwamna Ahmadu, ya bayyana […]

Musa Wada ya zama dan takarar Gwamnan Kogi a PDP

Injiniya Musa Wada, ya zama dan takarar Gwamnan Kogi a jam’iyyar PDP, a babban zaben Gwamnan jihar da za a yi ranar 16 ga Nuwamba 2019.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na masu neman takarar tsayawa a PDP zaben, Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ne ya sanar da hakan a yau.

Gwamna Ahmadu, ya bayyana sakamakon da cewa, Injiniya Musa Wada ya samu kuri’u 748 inda ya doke abokin takarar shi da ke kusa da shi a sakamakon, Abubakar Mohammed Ibrahim wanda ya samu kuri’u 710.