Musabakar Al-Kura’ni: An karrama Gwarazan Shekara na Jihar Kogi

Alaramma Abdulhalim Yunus da Hafiza Amina Idris Tahir sun zama Gwarazan Shekara na Gasar Alkur’ani na shekarar 2024 a Jihar Kogi.

Musabakar Al-Kura’ni: An karrama Gwarazan Shekara na Jihar Kogi

Wasu gwarazan musabakar AlKur’ani (Tsohuwar ajiya) Hoto: Muhammad Auwal Gusau da Nusaiba Shu’aibu Ahmad
Hoto: BBC Hausa

Alaramma Abdulhalim Yunus da Malama Amina Idris Tahir sun zama Gwarazan Shekara na Gasar Alkur’ani na shekarar 2024 a Jihar Kogi.

Alaramma Abdulhalim Yunus shi ne Gwarzon Shekara a bangaren masa ’yan Izu Sittin da Tafsiri a musabakar, a yayin da Malama Amina Idris Tahir ta zama Gwarzuwar Shekara a bangaren mata.

Mahaddata Al-Kur’ani 97 daga kananan hukumomi 21 na Jihar Kogi ne suka fafata a wanna musabaka, inda suke baje kolin karfin hadda da tajwidi da kuma sanin ma’anar ayayoyin Alkur’ani.

An shafe kwana biyar mahaddata Al’kur’ani suna gwada bajintarsu a wannan musabaka a matakai biyar.

Wadannan suka zama gwarazan shekara a kowane mataki su ne za su wakilinci Jihar Kogi a Gasar Musabakar Alkur’ani na Kasa da ke tafe.

Masabaqar wadda ita ce karo na 33 da Jihar Kogi ta gudanar garin Ife Olukotun da ke Karamar Hukumar Yagba ta Gabas ce ta zama mai masaukin baki.

A ranar Lahadi aka kammala tare da rufe musabakar, wadda aka fara a ranar 13 ga wannan wata na Nuwamba, ina alkakai sukan sanar da Alaramma Abdulhalim Yunus da Hafiza Amina Idris Tahir matsayin Gwarazan wannan shekara.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa