Musguna wa masu hijabi shiri ne na hana amfani da shi – kungiyar Jama’atu

kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bayyana cin fuska da wulakanta mata musulmi masu hijabi da ake yi a wadansu jihohi, musamman a Jihar Kano a matsayin shiri da wadansu ke yi domin ganin an hana yin amfani da hijabi a kasar nan. Babban Sakataren kungiyar, Shaikh Khalid Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a tattaunawarsa […]

Musguna wa masu hijabi shiri ne na hana amfani da shi – kungiyar Jama’atu

????????????????????????????????????

kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bayyana cin fuska da wulakanta mata musulmi masu hijabi da ake yi a wadansu jihohi, musamman a Jihar Kano a matsayin shiri da wadansu ke yi domin ganin an hana yin amfani da hijabi a kasar nan.
Babban Sakataren kungiyar, Shaikh Khalid Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya ta waya.
“Lallai wannan abin bakin ciki ne kuma ba za mu yarda da shi ba, a ce yau an dauki karan tsana an dora wa mata wadanda ke sanya hijabi, wanda Allah Madaukakin sarki ne Ya umarci musulmai mata su saka domin su rufe jikinsu, domin kawai wadansu da ba a san ko su waye ba suna amfani da shi wajen kai harin bam.
“Tun farko mu muna kallon abin ma kamar wani wasan kwaikwayo ne cewa wai ana kai hari da hijabi, domin, mu a ganinmu, wani salo ne da ake neman yi domin a ga an hana saka ko yin amfani da hijabi a kasar nan.
“Ai an yi lokacin da ake yi wa maza masu barin gemu wulakanci a kasar nan. Da zarar an gansu, sai a dauka wadansu ne da ke da hadari ta bangarEn tsaro, amma kuma idan wanda ba musulmi ba ne ya bar gemu babu mai cewa da shi uffan.”
Ya ci gaba da cewa, “Saboda haka wannan cin fuska da ake yi wa mata masu hijabi, ba za mu yarda da shi ba, domin kamar yadda na ce ne, wani shiri ne da muke gani kamar na wasan kwaikwayo domin a hana mata sanya hijabi a kasar nan.
“Muna kuma so mu janyo hankalin gwamnati cewa ko dokar kasa ba ta hana mutum sanya riga ko yin shiga irin ta addininsa ba, don haka muna janyo hankalin hukuma da kuma shugabannin jami’an tsaro da su umarci mutanensu su gaggauta daina tozarta mata saboda suna amfani ko suna sanye da hijabi. Domin gaskiya muna ganin wannan shiri ne kawai da ake yi domin tsangwamar mata musulmi da ke kasar nan, wanda kuma mu ba za mu yarda da hakan ba.”
Game da matakin da JamA’atu za ta dauka kuwa sai ya ce, “Za mu dauki matakin cigaba da jawo hankalin hukuma, domin wani lokacin kananan jami’an tsaro ke aikata wannan abin ba tare da sanin manyansu ba. Domin yana iya yiwuwa manyansu ba su ma san ana yin hakan ba. Sannan kuma za mu cigaba da sanya idanu domin ganin cewa an daina wulakanta jama’armu da sunan tabbatar da tsaro. Muna kuma jan hankalin mutane da su daina daukar masu hijabi da sunan ’yan ta’adda, domin yin hakan ba daidai ba ne da fatan Allah Ya cigaba da tsare mu da addininmu da kuma kasarmu baki daya,” inji shi.
Shi ma Shugaban dalibai Musulmi na Arewacin kasar nan (MSS), Ustaz Yusuf Arigasiyyu ya bayyana ra’ayinsa, inda ya ce akwai bukatar gwamnati ta hana masu neman wulakanta mata masu saka hijabi, domin a cewarsa, cigaba da yin haka na iya janyo rikici a kasar nan.
“Muna jan hankalin ma’aikatu da makarantu da ’yan kasuwa da jami’an tsaro  da ma duk wani dan Najeriya da ya sani cewa hijabi fa wajibi ne ga mace ta saka, idan aka ce za a tsamgwami masu sawa, hakan ba zai haifar wa kasar nan da da mai ido ba.
“Mu tunda aka ce mana masu hijabi ne ke kai harin bam muka fahimci akwai matsala, domin wadansu na zuwa kasashen waje suna fadin wai sun fi musulmi yawa a kasar nan, domin Turawa su ba su kudi, kuma Turawa idan suka zo kasar nan, sai su ga masu hijabi sun cika ko’ina. Shi ne ake neman yadda za a yi a hana saka hijabi ta hanyar yin amfani da wadansu masu sanye da hijabin suna ta da bam.
“Saboda haka mu ba mu ma yarda cewa wai musulmai ke tada bam din nan ba, don haka a dai bincika da kyau. Gaskiya abin da ake yi wa matan nan yana damunmu, kuma jami’an tsaro tunda da kudinmu ake biyansu, ya kamata su san abin yi, saboda mata na da ’yanci a Najeriya a matsayinsu na ’yan Najeriya, kuma a matsayinsu na Musulmai a Najeriya suna da damar saka irin tufafin da addininsu ya umarce su da sakawa ba tare da tsamgwama ba,” inji shi.
Rahotanni daga Jihar Kano na nuna cewa mata masu hijabi na tsorata wadansu mutane kasancewar a  makonnin baya an samu wadansu ’yan mata sun yi amfani da hijabi wajen kai hare-haren bam a jihar. Wannan ya sanya ake yi wa mata masu sanye da hijabi kallon tsoro, ta yadda idan sun tsaya sai a rika tambayarsu wa suke nema ko kuma me suke yi?
Aminiya ta gano cewa saboda tsangwama, yanzu akwai iyayen yara da ke shawartar ’ya’yansu mata da su rage ko su daina sanya hijabi, a maimakon haka su rika sanya gyale. Domin gudun wulakanci, yanzu mata masu hijabi sun rage fita zuwa unguwa.
 Haftsat I. Usman, wata daliba ce a daya daga cikin manyan makarantun jihar ta ce, “Wannan abin bakin ciki ne cewa muna fuskantar wannan matsalar, a ganina, wannan wata manakisa ce kawai ga Musulunci.”
Ta bayyana yadda mutane suka zura mata ido a lokacin da take jiran wani mutum a kan titin Kabuga a karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano. “Ina jiran mutumin ne, ni da kannena, kuma duk muna sanye ne da hijabi, sai muka lura mutanen da ke zaune kusa da wajen sun kura mana idanu da muka lura akwai damuwa a fuskarsu sai muka matsa kusa da su muka fada musu cewa akwai wanda muke jira ne.  Sai suka ce babu komai, amma dai duk da haka mun lura hankalinsu bai kwanta da tsayuwarmu a wajen ba,” inji ta.
Ita kanta Hafsat din ta bayyana yadda hankalinta ya tashi a lokacin da ta hango wata mata sanye da bakin hijabi ta tunkari inda suke tsaye. “Gabana ya fadi lokacin da na ga matar cikin bakin hijabi rike da jaka a kafadarta ta tunkari inda muke tsaye, hankalinmu ya kwanta ne kawai bayan ta wuce mu ba tare da wani abu ya faru ba,” inji ta.
A ganinta, ana amfani da hijabi wajen kai hari  ne domin a hana amfani da shi. Ta kuma cigaba da cewa, saka hijabi ga mace umarni ne daga Allah, kuma abu ne da ke nuna mata nagari.
Ta ce, “Mata na saka hijabi ne saboda bin umarnin Wanda Ya halicce su. Wanda Ya umarce su da rufe jikinsu da kuma kyansu daga mazajen da ba muharramansu ba. Wannan umarnin domin kare martabar al’umma ne, saboda zai taimaka wajen hana lalata a cikin jama’a,” inji ta.
Ta kuma tabbatar da cewa babu wani wulakanci ko cin fuska da zai hana su saka hijabi, sannan kuma a matsayinta na musulma, babu irin cin fuskar da za ta hana ta nuna kaunarta ga Musulunci. “Wannan abin da ke faruwa, ba zai sa mu yi wa Musulunci rikon sakainar-kashi ba, domin kuwa duk umarnin da Allah Ya bayar  Ya yi haka ne domin inganta rayuwar al’umma, ba ga musulmi kawai ba, saboda haka ina kira ga musulmi su cigaba da mutunta mata masu hijabi, duk kuwa da abin bakin cikin nan da ke faruwa a kasar nan. Allah ne kawai Zai iya kare mu daga mugayen mutane,” inji ta.
Wata ’yar kasuwa, Hajiya Hauwa Muhammad ita ma ta bayyana irin halin da ta shiga a lokacin da ta tunkari wadansu maza domin tambayarsu wani gida. Da farko suka ce ba su sani ba, amma da ta matsa musu da tambaya, sai duk suka gudu suka barta a tsaye ita kadai cikin mamaki.
 Wata mata kuma mai suna Hajiya Fatima Adamu, ta bayyana yadda ta wulakanta lokacin da take zaune a gaban wani ofis tana jiran ta karbi wadansu takardu, inda mutane daban-daban ke ta zuwa suna tambayarta wa take jira a wajen? “Gaskiya ban ji dadi ba, yadda mutane ke ta tambayata wa nake jira da alamar zargi. Ina tsaye duk na kosa wanda nake jira ya kawo min takardun domin in bar wajen,” inji ta.
Wata malamar makaranta kuwa da ba ta son a ambaci sunanta, ta nuna damuwarta ne a kan yadda ake ci wa mata masu hijabi fuska. “Ina mamakin yadda ake wulakanta mata masu hijabi don kawai wadansu mata na amfani da shi wajen ta’addanci. Ai wadansu na amfani da kayan sojoji wajen kai hare-hare, me ya hana ba za a rika gudu ko wulakanta sojoji idan an gansu ba?
Shi kuwa wani mazaunin Kano, Malam Muhammad Adamu bayyana wa Aminiya ya yi  cewa tuni ya rigaya ya bai wa matan gidansa shawarar su daina amfani da hijabi. “Na shawarce su da su daina saka hijabi saboda halin rashin tsaro da muke fama da shi a kasar nan, na ce su koma amfani da gyale,” inji shi.
Wata malamar addinin Musulunci, wacce ita ma ba ta son a ambaci sunanta, ta ce ba dole ba ne sai mata sun yi amfani da hijabi. A cewarta, akwai irin manyan mayafi, kamar Julba da mata za su iya amfani da shi wajen rufe jikinsu.
Shi ma Malam Isa Muhammad ya ce saboda wannan matsala mata na iya komawa yin amfani da gyaleluwa masu kauri da kuma girma irin wadanda mata ke amfani da su a baya a madadin hijabi. “Babu wanda ya ce dole sai mata sun saka hijabi irin wanda ake amfani da shi a yanzu. Suna iya amfani da manyan gyale masu kauri da iyayenmu ke amfani da su a baya,” inji shi.
Sai dai kuma ya gargadi mata da su guji yin amfani da gyale shara-shara, wanda zai nuna jikinsu, domin irin wadannan ba su dace da addinin Musulunci ba.