Musgunawa ‘yan Najeriya: Buhari ya tura wakilai zuwa Afirka ta Kudu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta damu matuka sakamakon harin da ake kaiwa ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu, yayin da Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya yi Allah wadai da harin da ‘yan kasar suke kaiwa ‘yan kasashen waje. Shugaba Buhari ya bada umarnin tura wakilan Najeriya na musamman don tattaunawa da jami’an kasar […]

Musgunawa ‘yan Najeriya: Buhari ya tura wakilai zuwa Afirka ta Kudu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta damu matuka sakamakon harin da ake kaiwa ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu, yayin da Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya yi Allah wadai da harin da ‘yan kasar suke kaiwa ‘yan kasashen waje.

Shugaba Buhari ya bada umarnin tura wakilan Najeriya na musamman don tattaunawa da jami’an kasar Afirka ta Kudu akan dakile hanyoyin musgunawar da ake yi wa ‘yan Najeriya.

‘Yan kasar Afirka ta Kudu sun dade suna kaiwa baki ‘yan kasashen waje hari duk da gargadin da gwamnatin kasar ke yi game da abin da rikicin zai haifar.

‘Yan Najeriya da dama nata kiraye kiraye kan kauracewa amfani da kayayyakin Afirka ta Kudu sakamakon kin jini da wasu ‘yan Afrika ta Kudun ke nuna wa ‘yan Najeriyar da sauran kasashe mazauna kasar.

Wasu daga cikin kamfanonin Afirka ta Kudu da ke zaune a Najeriyar sun hada da: kamfanin sadarwa na MTN da kuma shagunan siye da siyarwa na Shoprite da kuma kamfanin talabijin na DSTV.