Musulmai da Kiristoci sun yi addu’ar rokon ruwa a Maiduguri

An yi addu’ar ce domin rokon ruwa da zaman lafiya

Musulmai da Kiristoci sun yi addu’ar rokon ruwa a Maiduguri

Al’ummar Musulmai da Kiristoci sun gudanar da addu’o’i na musamman domin rokon ruwan sama da dauwamammen zaman lafiya a Jihar Borno.

Dubban mutane ne a suka fita a Maiduguri, babban birnin Jihar, domin gudanar da addu’o’in duba da yankewar ruwan saman da aka samu a yankuna da dama na Jihar.

Aminiya ta rawaito cewa yayin da mabiya addinin Islama suka gudanar da sallar Juma’a a masallatai daban-daban a ranar Juma’a, Kiristoci mabiya dariku daban-daban sun hallara a cocin First Baptist da ke Maiduguri, domin gudanar da nasu addu’o’in.

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi, da jami’an Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN)  sun bukaci mabiya da su yi addu’ar Allah ya kawo dauki kan karancin ruwan sama da ake fama da shi a sassa da dama na Jihar.

Mai martaba Shehu ya kuma umarci dukkan Hakimai da Bulamomi hadi da Lawanai a fadin Jihar da su hada kansu domin tallafa wa mabukata, marayu da nakasassu a wani bangare na addu’o’in.

Ya kuma shawarci dukkan iyaye da su shawarci ’ya’yan su da su guji aikata fasikanci, munanan dabi’u da suka hada da shaye-shayen miyagun kwayoyi, sannan ’yan kasuwa su ji tsoron Allah wajen gudanar da sana’arsu ta halal.

A jawabinsa na kwadaitarwa a lokacin taron ga Kiristoci a cocin Baptist, Shugaban CAN na Jihar,  Rabaran John Bakeni, ya bukace su da su nemi fuskar Allah kuma su bi hanyoyinsa wajen mu’amalarsu don yin bishara.

Haka kuma, Bishop na cocin Anglican na Maiduguri, Rabaran Emmanuel Morris, ya kuma yi addu’ar Allah ya bai wa Jihar zaman lafiya da ruwan sama mai albarka domin amfanin gona ya yawaita.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya