Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya

Sun zargi wasu manyan yankin da cin gajiyar rikice-rikice, nuna wariya ga Musulmi a masarautu, ƙirƙirar adadin jama’a saɓanin gaskiya da kuma yi wa gwamnati barazana

Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya

Kaduna

Ƙungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudancin Kaduna mai suna ‘Concerned Muslim Ummah’ ta zargi wasu manyan mutane a yankin da haifar da rarrabuwar kawuna da kuma juya tarihi domin cimma manufofin siyasa.

A taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna, ƙungiyar ta yi watsi da iƙirarin cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci ne kaɗai.

Ta jaddada cewa Musulunci ya daɗe da wanzuwa a yankin tun ƙarnoni da suka gabata, inda ta ce Musulmi sun kai kusan kashi 40 cikin ɗari na al’ummar yankin.

Ƙungiyar ta ce tashe-tashen hankula kamar na Zangon Kataf a 1992 da rikicin bayan zaben 2011 sun tabbatar da cewa rikice-rikicen yankin ba wai na yanzu ba ne.

Ta kuma zargi wasu daga manyan yankin da cin gajiyar rikice-rikice, nuna wariya ga Musulmi a masarautu, ƙirƙirar alƙaluman yawan jama’a da kuma yi wa gwamnati barazana.

Ta kuma jaddada rawar da Musulmi suka taka a zaɓuɓɓukan baya, ciki har da goyon bayan da suka bai wa Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Yayin da ta yaba da salon mulkin haɗin kan gwamnan, ƙungiyar ta buƙace shi da ya ci gaba da yin taka-tsantsan daga siyasar barazana.

Haka kuma ta kira kafafen yada labarai da su riƙa bayar da rahoto bisa gaskiya tare da jan hankalin al’umma su guji siyasar rarrabuwar kawuna.

A ƙarshe, ƙungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Kaduna.