Musulmi 82 sun lashe zabe majalisa a Amurka
Musulmi 82 sun yi nasara a zaben rabin zango na Majalisun dokokin kasar Amurka da aka gudanar ranar Latata.
Musulmi 82 sun yi nasara a zaben rabin zango na Majalisun dokokin kasar Amurka da aka gudanar ranar Latata.
Wasu daga cikinsu sun lashe kujerun Majalisar Tarayya, 43 kuma kujerun majalisun dokokin jihohi, ciki har da wadanda suka yi tazarce a 2018 da 2020 — Jihar Minesotta ce ta fi yawan ’yan Majalisa Musulmi, sai Georgia.
“Nasarar da Musulmi ke samu a zabuka a majalisun dokoki na kara mana kwarin gwiwa, kuma ya nuna Musulmi na kafa ginshiki mai karfi domin samun nasara a zabe,” in ji Muhammad Missouri, Shugaban Cibiyar Jetpac, wadda ke ba wa ’yan takara Musulmi horon shiga zabe.
Ya bayyana wa taron Cibiyar Musulmai ta Amurka cewa, “’Yan Majalisa ne ka da ta cewa kan tsare-tsaren ilimi da muhalli da suransu da kuma hare hakki, saboda haka yake da muhimmaci mu samu wakilci a bangaren.”
Musulmin da suka ci zaben sun hada da maza da mata da matasa, yawancinsu daga jam’iyyar Democrat, sauran kuma daga Republican.
Musulmi 145 ne dai suka fito takara a zabukan majalisun dokokin kasar.
Akwai kuma wadanda suka yi nasarar samun mukamai ko cin zabe a matakai daban-daban na shugabancin yankuna da makarantu a matakan kananan hukumomi.