Musulmi a dukufa da ayyukan gina al’umma
A bisa ga al`ada kuma shekaru aru-aru, an san al`ummar Musulmi da kokarin gina masallatai da makarantun Islamiyya, musamman tsakanin masu hali, a zaman tasu gudummuwar bunkasa addinin Islama. Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da irin karantarwar maluman farko a kan yin wadancan ayyuka biyu da akasari maluman kan danganta su da ayyukan ibada […]
A bisa ga al`ada kuma shekaru aru-aru, an san al`ummar Musulmi da kokarin gina masallatai da makarantun Islamiyya, musamman tsakanin masu hali, a zaman tasu gudummuwar bunkasa addinin Islama. Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da irin karantarwar maluman farko a kan yin wadancan ayyuka biyu da akasari maluman kan danganta su da ayyukan ibada na sadaka mai gudana, wato ayyukan da ko bayan ran mutum, za a rika rubuta masa lada, har ya zuwa ranar tashin Alkiyama. Irin wadannan ayyukan alheri da al`ummar musulminmu suke yi, har gobe don neman waccan lada, sun hada da aurar da budurwa sadaka (kodayake wannan ya yi matukar raguwa, a kan fahimtar addini da ake ta kara samu), da kuma gina rijiya ko dasa bishiya da dai makamantan ayyukan alheri.
Akasarin irin wadannan masallatai da makarantun islamiyya za ka tarar, wadanda suka gina su, su ke tafiyar da su, a wasu wurare kuma al`ummar Annabi ke rungumar da dawainiyar tafiyar da su, inda ko aka samu al`umma suka taru suka gina, za ka tarar su dai jama`ar sun ci gaba da kulawa da su daidai da zamani. A takaice dai ka iya cewa Alhamdulillah daga irin wannan gudummuwa da al`ummar Musulmi suke bayarwa a cikin birane da karkarar wasu jihohin Arewa, akan ayyukan da suke ganin tamfar su kadai ne ayyukan bunkasar addinin Islama. Sabanin zamantakewar abokan zamanmu na kudancin kasar nan da suka gaji duk wani aikin ci gaban al`umma da za su yi, to kuwa wajibi ne ga dukkan dan wannan yanki yana cikin yankin ne da zama ko baya, to kuwa a tilas dinsa ya kawo ta sa gudummar, domin da ita ce, mutanensa za su ce, sun more ko kuma ya fara biyan bashin yadda al`ummarsa suka tallafa wa rayuwarsa, tun yana karami.
Abokan zamanmu sun yi mana fintikau a dukkan wasu ayyukan taimakekeniya, ta haka makarantunsu na Firamare da na Sakandare, na al`umma da na Hukumomi suke kan-kan-kan da juna, ta fannoni da yawa, ko ingancin koyarwa da sauransu. Ta irin haka yanzu mutanen kudancin kasar nan suke da manya makarantu irinsu jami`o`i da asibitoci da hanyoyin samar da ruwan sha da sauran ayyukan ci gaba da al`ummarsu suka gina musu, kar ka yi batun gina Majami`u.
A takaice dai a lokacin da har yanzu al`ummar ta musulmi suke zuba idanu don samun kusan komai daga mahukunta, takwarorinmu na kudu sun yi nisa wajen sama wa kansu irin wadannan ababe. Dole ne mu fahimci cewa, inda duk al`umma ta rungumi taimaka wa kanta da kanta, to, za ka tarar tana matukar kula da wadannan ayyukan, kuma komai za a yi a kan su, kowa na da rawar da zai taka, sabanin Alhaji wane ya gina, ya kuma rika tafiyar muku, ku kuma kun zama ci ma zaune. Don haka ashe ba karamar fa`ida ba ce al`umma su rika jiibantar al`amurransu da kansu, musamman yanzu da gwamnatocinmu ke cewa ayyuka sun yi musu yawa.
Mai karatu ba wani abu ya sa na yi maka wannan dogon bayani a wannan makala ta yau ba, sai don in kawo maka labarin wasu ayyukan alheri biyu da na ga wasu al`umma sun yi, ko kuma wani mutum ya yi a garuruwan Kano da Funtuwa da ke cikin Jihar Katsina. Bari in fara da Kwalejin Kimiyar Lafiya ta al`ummar Musulmi da ke cikin garin Funtuwa, Kwalejin da wasu matasa daga Da`awar kungiyarsu ta dalibai Musulmi ta kasa, wato MSSN suka kafa a shekarar 1999, yau shekru 15. Kwalejin da ya zuwa yanzu ta yaye dalaibai 1,300, a fannoni kimiyar kiwon lafiya guda hudu da take koyarwa, wato ma`aikatan kiwon lafiyar al`umma da na tsaftar muhalli.
A yanzu kuma maganar da ake yi, tana da dallibai 550 daga jihohin kasar nan 19, ciki kuwa har da na kudanci, baya ga Malamai da sauran ma`aikata da suka kai 45, ta na kuma da niyyar fara wani karatun akan ilmin lafiyar hakori da na harhada magunguna, da kuma fara bayar da babbar shaidar difuloma akan fannonin da ta dade tana gudanarwa. kananan Hukumomin Funtuwa da Malumfashi da tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Katsina kuma tsohon Jakadan kasar nan a kasar Saudiyya, Ambasada Abdullahi Garba Aminci, da Dokta Tukur Abdullahi suke cikin sahun farko na hukumomi da mutanen da suka assasa kafuwar Kwalejin, ta hanyar bayar da damar fara samun shahada ko matsugunni, kuma har yanzu suna kai. Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau ita ma ta kai dauki Kwalejin ta fannoni daban-daban tun a shekarar 2004, sai uwa uba mai girma Sarkin Maska Hakimin Funtuwa Alhaji Sambo Idris Sambo,kuma shugaban Hukumar Amintattun Kwalejin, wanda ya dora daga inda mahaifinsa, marigayi Sarkin Maska Alhaji Idris Sambo ya tsaya cikin dawainiya da Kwalejin, sai kuma mutanen yankin da sauran al`ummar musulmi na kusa da na nesa da suke tsaye wajen bada tasu gudummuwar tafiyar da Kwalejin.
Kadan ke nan akan wannan Kwaleji, wadda ba sai na fadi irin matukar muhimmancin da take da ita ba, cikin ganin kyaututuwar samun masu ilmin kiwon lafiya a matakin farko, wanda masu ilminsa, ake da matukar bukata, ta yadda za su rika tallafa wa rayuwar mutanen karkara da suke fama da karancin rashin kiwon lafiya.
Aiki na biyu kuma shi ne Cibiyar ko’ince Gidauniya da ake kira Darus Sunnah, da shararren dan kasuwar man fetur din nan Alhaji Auwalu Rano ya gina a unguwa uku, da ke kewayen birnin Kano, aka kuma bude ta watan Satumban 2010. Wannan Cibiya da take bene mai hawa daya, ta kunshi dakunan shirya da daukar shirye-shiryen karatuttuka na addinin musulunnci, walau don Radiyo ko Telebijin, da makeken dakin taro da na karatu da ofisoshi da masallaci da bandakuna da makarantar Islamiyya da rijiyar burtsatse da dai sauran wurare.
Wani babban abin jin dadi bai wuce irin yadda aka kawata wannan Cibiya da dukkan abin da zuciyar mai karatu za ta iya habarto masa, na wala-alla na`urorin aikin jarida ko na ofis ofis, da zai iya tunani. Babbar karantarwar da na san ana shiryawa a wannan Cibiya, kuma ta game kasa ko ma duniya shi ne shirin nan na “TAMBAYA MABUdIN ILMI” da Sheikh Aminu Ibrahin Daurawa ke shiryawa, da babban dan kasuwar nan na Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai ke daukar nauyinsa.
A takaice, akwai bukatar musulmin wannan yanki, walau a kungiyance ko a daidaiku, su fara mayar da hankali wajen samar da irin wadannan aikce-aikace, ta yadda za mu rika tafiya da zamani. Allah Ya ba mu ikon yi.