Musulmi a Kamaru sun yi haramar Sallar layya

A gobe Asabar ne take Sallah a Kamaru kamar yadda hakan zai kasance a sauran kasashen duniya , dalili da haka hankulan jama’a suka karkata wajen shirye-shiryen zuwar ranar.  A kasuwar sayar da tumakai ta birnin Yaounde, ana shigo da raguna da dama daga arewacin kasar duk shekara, sai dai a bana akwai karancin  masaya […]

Musulmi a Kamaru sun yi haramar Sallar layya
Musulmi a Kamaru sun yi haramar Sallar layya

A gobe Asabar ne take Sallah a Kamaru kamar yadda hakan zai kasance a sauran kasashen duniya , dalili da haka hankulan jama’a suka karkata wajen shirye-shiryen zuwar ranar.  
A kasuwar sayar da tumakai ta birnin Yaounde, ana shigo da raguna da dama daga arewacin kasar duk shekara, sai dai a bana akwai karancin  masaya ragunan. Ana iya cewa sai dai masu hannu da shuni ne suka fi sayan ragunan, wasu kuma idan sun ziyarci kasuwar domin neman sanin farashin raguna da niyyar dawowa ranar Sallah domin su saya, ko da farashin ka iya yin kasa.
A yanzu dai rago mafi sauki ana samunsa kan CFA 100,000 zuwa CFA 300,000 kwatankwacin Naira 40,000 zuwa Naira 120,000.
Game da sutura kuma akasarin jama’a za su yi amfani da wanda suka sanya ne a Sallar azumi. Wasu masu hannu da shuni kuma suna sake wa iyalansu sutura, a dalilin haka wasu teloli suka dawo da kwana a cikin shagunansu domin tserereniyar da suke yi da lokaci ganin cewa Sallar na karatowa, sa’annan kuma ayyuka sun yawaita. A takaice dai wannan Sallar kamar sauran salloli take wato ta zo wa jama’a ne a cikin wani hali na rashin kudi, komai ya yi tsada sakamakon karin kudin man fetur. Sa’annan kuma wasu kayayyakin da suke zuwa daga arewacin kasa bayan sun shigo daga Najeriya sun yi wuya, sakamakon rashin tsaro da kuma rufe iyakokin Kamaru da Najeriya da hukumomi suka yi a dalilin bullar cutar Ebola. Lamarin da ya sa harkoki suka tsaya cak.