Musulmi da Kirista sun yi bikin Maulidi tare a Bauchi

Musulmi da Kiristan Unguwar Yalwan Tudu da ke Bauchi sun gudanar da bikin Maulidi tare domin samar da maslaha tsakanin juna daga irin rashin fahimtar juna da aka rika samu a tsakanin jama’ar unguwar a baya. Maulidin wanda kungiyar Harkar Musulunci ta almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky ta shirya ya samu halartar manyan fastoci da Rabaran-Rabaran […]

Musulmi da Kirista sun yi bikin Maulidi tare a Bauchi
Musulmi da Kirista sun yi bikin Maulidi tare a Bauchi

Musulmi da Kiristan Unguwar Yalwan Tudu da ke Bauchi sun gudanar da bikin Maulidi tare domin samar da maslaha tsakanin juna daga irin rashin fahimtar juna da aka rika samu a tsakanin jama’ar unguwar a baya.
Maulidin wanda kungiyar Harkar Musulunci ta almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky ta shirya ya samu halartar manyan fastoci da Rabaran-Rabaran da ke jagorancin kungiyoyin addinin Kirista da majami’u, wadanda suka nuna gamsuwa da jin dadinsu game da gayyatar da suka ce ta dinke matsaloli masu yawa da aka yi fama da su a baya.
Jagoran kungiyar ’yan uwa Musulmi Malam Ahmad Yusuf Yashi ya ce a kowace shekara suna shirya irin wannan Maulidi a unguwar inda ake isar da sakon da ya bambanta da sauran wurare saboda dinke rashin fahimtar juna da aka yi fama da ita a baya wacce ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya mai yawa, kuma ana ganin alherin yin hakan a halin yanzu.
Ya ce Musulunci ba ya tilasta wa wani cewa dole ya shiga cikinsa, amma yana bayani da zantukan baki domin nuna misalin da idan mutum ya gamsu zai shiga Musuluncin. Ya ce saboda ’yan uwantaka ta zamantakewa da ake da ita a tsakani da ’yan uwantaka ta addini ko dabi’a da halitta kuma saboda Allah Ya haramta zalunci ko haifar da fitina a tsakanin juna da Ya hada su zama wuri guda, bai kamata a rika samun fitina ba. Ya ce babu abin da ya fi komai dadi kamar zaman lafiya. “Ganin halin da aka shiga ya sa muka bullo da gayyatar Kiristoci zuwa bikin Maulidin domin samun fahimtar juna da isar da sakon karfafa zaman lafiya a tsakanin Musulmi da Kirista,” inji shi.
A jawabin Shugaban kungiyar Kiristoci (CAN) reshen karamar Hukumar Bauchi Rabaran Yahaya Madaki ya bayyana jin dadi game da gayyatar da ake yi musu. Ya ce sai da zaman lafiya kowa zai ji dadin zama a inda yake. Ya ce addinin Kirista tushensa Annabi Ishak dan Ibrahim, Musulunci kuma ya taso daga Annabi Isma’il dan Annabi Ibrahim kuma duk Annabawa suka kawo addinan. Don haka akwai bukatar a zauna tare a fahimci juna don samun ci gaba da kuma zama jagora ga rayuwa.
Ya ce addinan biyu sai sun hada hankali wuri guda sun karantar da yara da matasa zaman lafiya da muhimmancinsa za a samu zaman lafiya. “Amma idan an karantar da fitina za a samu fitina, fitina kuma za ta damu kowa. Don haka ya kamata kowa ya yi hattara ya sani zaman tare shi ne mafi alheri daga rigima,” inji shi.
An gabatar da jawabai masu yawa da nasihohi da kuma faretin daliban makarantar Fudiyya da ke Bauchi a wajen taron Maulidin.