Musulmi da Kiristoci ’yan uwan juna ne – Papa Roma
A ziyarar kwanaki biyu da ya kai Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Shugaban darikar Katolika Papa Roma Francis ya kai ziyara unguwar PK5 da ta kunshi mafi yawan Musulmi a Bangui babban birnin kasar.Baya ga haka ya shiga babban masallacin garin, inda ya tunatar da Musulmi da Kiristoci cewa su ’yan uwan juna ne, saboda haka ya […]
A ziyarar kwanaki biyu da ya kai Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Shugaban darikar Katolika Papa Roma Francis ya kai ziyara unguwar PK5 da ta kunshi mafi yawan Musulmi a Bangui babban birnin kasar.
Baya ga haka ya shiga babban masallacin garin, inda ya tunatar da Musulmi da Kiristoci cewa su ’yan uwan juna ne, saboda haka ya kamata su yi Allah-wadai da ramuwar gayya, su nisanci tashe-tashen hankula da kuma kyashi da juna.
Papa Roman ya bayyana haka ne a gaban dubannin Kiristoci da Musulmi da suka yi tururuwa zuwa masallacin domin karbar bakuncinsa karkashin jagorancin babban limamin birnin Bangui Malam Nehedi Tidjani. Sai dai Shugaban Darikar katolikan bai yi wani jawabi mai tsawo ba a masallacin, a dalilin kasancewarsa a masallacin na wani gajeren lokaci ne kimanin mintuna 30.
Kodayake, ya yi addu’o’in fatan sake maido da zaman lafiya a kasar. Baya ga masallacin kuma, Papa Roma ya ziyarci filin wasan kwallo a birnin Bangui, inda aka kiyasta mabiya addinin Kirista dubu 20 ne suka halarci addu’o’in da ya yi na tsawon sa’o’i uku.
Gabannin Papa Roma ya shiga unguwar PK5 an kawar da duk wasu shingayen da mayakan sa-kai na Anti-Balaka suka kafa a ciki da wajen unguwar. Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya da kuma na Faransa su ne suka jagoranci ayyukan samar da tsaro a yankin. Hakan ya ba da damar gudanawar abubuwan da aka shirya ba tare da an fuskanci wata matsala ba.
Har ila yau, ganin irin hadin kai na zahirin da ya fito fili a tsakanin Musulmi da kuma Kiristoci lokacin karbar bakuncin Papa Roma, tarin jama’a sun sanya kaunar ganin cewa ziyarar ta Francis za ta zama sanadiyyar samun magance baraka da kuma kyamar juna da ta wanzu a tsakanin mabiya addinan biyu.
Sai dai wannan ya zama na gajeren lokaci ne kawai, saboda bayan Papa Roma ya kammala ziyararsa a kasar a ranar Litinin. Washegari Talata ne aka hallaka wani Musulmi a unguwar PK5 yana tsaye kusa da Masallacin Ibni katab. Kodayake, rahotanni sun ruwaito shugaban ‘yan kasuwar wannan unguwar yana cewa wanda harin ya shafa mutum ne bai ji ba, bai gani ba.