Musulmi da yankin Arewa na cikin kunci – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ada Abubakar ya koka kan yadda Musulmi da yankin Arewa suke cikin kunci da matsala da fuskantar barazana iri-iri, inda ya ce duk lokacin da wani abin batanci ya faru a kasar nan sai kawai a lakaba wa Musulmi.Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da […]

Musulmi da yankin Arewa na cikin kunci – Sarkin Musulmi
Musulmi da yankin Arewa na cikin kunci – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ada Abubakar ya koka kan yadda Musulmi da yankin Arewa suke cikin kunci da matsala da fuskantar barazana iri-iri, inda ya ce duk lokacin da wani abin batanci ya faru a kasar nan sai kawai a lakaba wa Musulmi.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yaa karbi bakuncin Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar wanda ya kai masa ziyarar mubayi’a a fadarsa.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce “Mun sha fadi cewa Musulmi ba ’yan ta’adda ba ne a ko’ina suke balle na Najeriya da suka shahara da kamun kai da yakana da sanin abin da ya kamata.”
“Me ya sa za a ce idan dan Arewa ya je wata jiha sai an ba shi katin shaida kafin zama a jihar, alhali kasarsa ce?  Me ya sa haka? Ya kamata mu bincika, kada wannan lamari ya kara kazancewa, kowa ya kamata ya san duk dan kasa yana da ’yancin zama a inda yake bukata matukar shi ba batagari ba ne,” inji Sarkin Musulmi.
Ya shaida wa Sarkin Gombe cewa: “Sabon Sarki ka zo a lokaci mai wahala wanda a yanzu ne al’ummar Musulmi ke bukatar taimakon sarakunansu fiye da inda aka fito domin ceto su cikin halin kuntatawa da suke ciki. Saboda haka nake bukatar ka ja damara domin aiki ne a gabanka sosai, jama’arka kai ne za ka yi musu hidima ba su ne za su yi maka ba, kamar yadda muka karanta a littattafan magabatanmu da muke shirin bugawa don raba wa ga masarautunmu da Mujaddadi danfodiyo ya ba rubuta.”
Ya shaida wa sabon Sarkin cewa sun yi zaman soyayya sosai da mahaifinsa kan gaskiya da tsoron Allah don haka shi ma ya yi koyi da shi, “Ba wani mutum da zai iya yi maka wani abu sai da son Allah, don haka ka dogara da Shi, domin Shi ne Ya ba ka mulki ba ta hanyar kowa ba, kada wani ya ce ta hanyarsa ka samu, to ba haka ba ne, ganin damar Ubangijinka ne, Shi ne Ya dora ka a karaga,” inji Sarkin Musulmin.
Ya yi alkawarin yin aiki da sabon Sarkin Gombe domin ciyar da al’ummar Musulmi gaba a kasar nan. “Za mu yi aiki da kai kamar yadda muka yi da mahaifinka domin shi mutum ne mai gaskiya kafin rasuwarsa ya jagoranci wani kwamitin samo hanyoyin sasanta Fulani makiyaya da kabilun jihohin Nasarawa da Benuwai, wanda ya mika mana rahoton kuma muna shirin mika shi ga gwamnoni domin aiwatarwa, don haka muke son ka jajirce ka gaji mahaifinka wajen gaskiya da amana, ba za ka samu wannan nasarar ba sai ka ji tsoron Allah Shi kadai, ka daina jin tsoron kowa,” inji shi.
Da farko sabon Sarkin Gombe ya gode wa Mai alfarma Sarkin Musulmi kan damar da ya ba shi ta kawo ziyarar mubayi’a ganin wannan daular daya ce da ta kafu fiye da shekara 200 da suka gabata. Ya ce, tsakanin masarautar Gombe da ta Sakkwato akwai soyayya mai karfi sosai, ganin yadda Malam Buba Yero ya bar Gombe ya je Sakkwato ya zauna shekara 12 sa’annan Mujaddadi danfodiyo ya mayarda shi domin karantar da mutane da jagoratarsu.