Musulmi ku daina sayan kayan Faransa – ’Yan Saudiyya

Wasu ’yan kasar Saudiyya sun yi kira ga al’ummar Musulmi da su kauracewa sayan kayayyakin kamfanonin kasar Faransa domin zanen batancin da aka wallafa a jaridar barkwancin kasar ta Charlie Hebdo. A wasu sakonni da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun bayyana haka: “Ya dace mu kaurace wa kayayyakin kamfanonin abinci da kuma na […]

Musulmi ku daina sayan kayan Faransa – ’Yan Saudiyya
Musulmi ku daina sayan kayan Faransa – ’Yan Saudiyya

Wasu ’yan kasar Saudiyya sun yi kira ga al’ummar Musulmi da su kauracewa sayan kayayyakin kamfanonin kasar Faransa domin zanen batancin da aka wallafa a jaridar barkwancin kasar ta Charlie Hebdo.

A wasu sakonni da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun bayyana haka: “Ya dace mu kaurace wa kayayyakin kamfanonin abinci da kuma na turaren kasar Faransa domin durkusar da tattalin arzikin kasar saboda ba su da mu da Musulmi ba. Wannan shi ne matakin da ya dace mu dauka domin kare addininmu da kuma Manzon Allah.”
Sauran sakonnin da aka sanya sun hada da wadanda suke bayyana sunayen kayayyakin kamfanonin kasar, wadanda mazauna Saudiyyar za su kauraceawa saya. Wani dan kasar mai suna Adel Hassan, ya ce zai kauracewa kayayyakin. Ya kara da cewa: “Idan duka masaya kayayyakin za su yi hakan, wannan na nufin cewa kamfanonin za su yi asara mai dimbin yawa ke nan. Kuma matakin zai sa kasar ta shiga taitayinta,” inji shi.
Hakazalika, a kasar Jordan ma an samu irin wannan kiraye-kiraye a shafukan sada zumunta. Masu hakan sun ambaci sunan kamfanin gidajen man da iskar gas na Total, a matsayin daya daga cikin kamfanonin da za a kauracewa. Kuma a halin yanzu wadanda ke jagorantar kamfen din sun ce sun samu goyon bayan mutum fiye da dubu hudu daga shafin Facebook. Yayin da suka ce hakan zai kara matsin lamba ga kasar Faransa wajen kawo karshen zanen batanci ga Manzon Allah, kamar yadda suka bayyana.
Wani jami’in hulda da jama’a mai zaman kansa ya bayyana wa jaridar Arab News cewa, “akwai kamfanonin kasar Faransa da dama a
yanzu da suka fara daukar hayan kwararrun jami’an hulda da jama’a wajen lalubo dabarun maganin matsalar da kauracewa sayan kayayyakin za ta haifar. Hakazalika, akwai wasu kamfanonin kasar a yankin Tekun Fasha da suka fara Allah-wadai da zanen batancin, a wani mataki na gyara kasuwarsu tsakankanin al’ummar Musulmi,”inji shi.