Musulmi na cikin tsanani a Afirka ta Tsakiya

Halin rayuwar jama’a na dada tsananta a jamhuriyar tsakiyar Afrika sakamakon kauracewar da tarin musulmai da ake gallaza musu suke yi. Wadanda suka rage a cikin kasar ma suna fuskantar tsadar rayuwa, a dalilin cewa akasarin musulmin kasar da kuma baki ‘yan kasuwa ne. Lamarin da ya sa ‘yan tawayen Anti-Balaka suke ta ci gaba […]

Musulmi na cikin tsanani a Afirka ta Tsakiya

Halin rayuwar jama’a na dada tsananta a jamhuriyar tsakiyar Afrika sakamakon kauracewar da tarin musulmai da ake gallaza musu suke yi. Wadanda suka rage a cikin kasar ma suna fuskantar tsadar rayuwa, a dalilin cewa akasarin musulmin kasar da kuma baki ‘yan kasuwa ne. Lamarin da ya sa ‘yan tawayen Anti-Balaka suke ta ci gaba da rushe kantuna da gidajen Musulmi domin su samu wani abin amfani. A inda kuma ake samun abin sayarwa farashin komai ya karu, wato ya rubanya da kusan kashi dari cikin dari. Alal misali karamar litan ruwan sha ta kai CFA 700 kwatankwacin kundin Yuro daya da  wasu burbudi.
Amma kuma duk da hijirar da Musulmi suka yi izuwa makwabtan kasashe, a cikin unguwarsu ta KM5 a kasuwar Sambo ake yin katarin samun wasu kayasn masarufi. Amma kuma a ko wace wayewar gari rayuwa dada kamari take yi. Ga shi kuma kusan komai ya tsaya cik. A cikin wata sanarwar da kungiyar agaji ta Odfam ta kasar Britaniya ta wallafa, ta koka kan bullowar yunwa a wannan kasar sakamakon ficewar da Musulmi wadanda aka kiyasta yawansu akan 15 cikin 100 na daukacin al’ummar kasar mai yawan mutane miliyan hudu suke yi. Ta nuna cewa kuma wannan yunwar ka iya shafar duban mutane da kuma yake-yaken kabilanci da kuma na addini suka daidaita kansu. Akalla mutane dubu 10 ne ake kiyassin cewa suka yi asarar rayukansu tun lokacin da wannan rikicin ya fara har izuwa yanzu. a yayin da kuma sama da mutane miliyan guda ne suka kaurace daga matsuguninsu. Don haka kungiyar ta ce abin da ya kamata a yi shi ne na tabbatar da tsaro ta hanyoyin shigowa kasar, musamman daga Kamaru, inda daga nanne akasarin kayayyakin kasar ke shigowa.
Shi kuwa Kwamandan dakarun MISCA na kungiyar Hadin kan Afrika, Martin Tumenta Chomu ya ce sau uku a cikin mako guda dakarun suka rika rako jerin gwanon manyan motoci masu dauke da kaya daga Kamaru izuwa Jamhuriyar Tsakiyar Afrika. Rashin zirga-zirgar motoci a tsakanin kasashen biyu ya kai ga Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar dinkin Duniya (WFP) ta kasa tafiyar da aikinta kamar yadda ya kamata. Manyan motocinta 23 ne dauke da ton-ton na abinci 27 suka kasa isa cikin birnin Bangui kusan wata guda domin kai agajin abinci. an hada su da ayarin sojoji masu tabbatar da tsaro na MISCA, inda suka samu shiga birnin a karshen makon jiya.
Su kuwa ‘yan tawayen Anti-Balaka masu goyon baya ga hambararren Shugaban kasa Francois Bozize na yunkurin ganin Gwamnatin Catherine Samba Panza ta shigar da su ayarin sojojin kasar. Su Anti-Balaka (masu nuna kishi da adda), wadanda su ne suke kai wa Musulmi hari, sun samu kafuwa ne kamar yadda suka fada domin shawo kan azabar da hadakar Seleka, wadda ta bai wa Shugaban kasar wanda ya yi murabus Michel Djotodia damar darewa kan mulki. A yanzu kuma dai wata takkadama ce take kunno kai game da yadda sojojin kasashen ketare wadanda ke aikin tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika suke yi. A yayin da al’ummar Musulmi suke  zargin sojojin kasar Faransa “Sangaris” da nuna goyon baya ga kristoci, suma kristocin cewa suke yi sojojin kasar Chadi na taimaka wa Musulmi da makamai domin su yake su.
Mafi yawan jami’an gwamnati sun kaurace wa ma’aikatunsu.
Ita kuwa shugabar kasar ta wucin gadi, Catherine Samba Panza na dada ci gaba da kira ga ‘yan kasar da su hada kansu, su ajiye makamai, su yi tunani, ta yadda za su farfardo da tattalin arzikin kasar. Ana iya cewa kuma wannan kira nata bai samu shiga kunnuwan ‘yan Anti-Balaka ba, wadanda suke ci gaba da rusa gidajen jama’a da masallatai. A yanzu dai an kiyasta cewa sama da masallatai 50 ne ‘yan Anti-Balaka suka rusa, hadi da tarin gidajen kwanan jama’a. Lamarin da ya sa a yanzu wasu Musulmin suke zaman gudun hijra a wasu masallatai, kafin su damar shigewa zuwa wasu wurare daban. Wannan al’amarin bai tsaya kawai a babban birnin kasar ba, wato Bangui, ya kai ga wasu birane kamar su Bouar da kuma Bocaranga.