Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau

A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya.

Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau

A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya.

Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron.

Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya?

Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ce ta shirya wannan taro. An gayyaci duk ƙungiyoyin Musulunci; kuma muna cikinsu.

Don haka, muna ganin ya wajaba a gare mu mu gaya wa dubban masu kallo da mabiyanmu cewa wannan shi ne manufar wannan taro da zai tattar makaranta da mahaddata Al-ƙur’ani Mai Girma ta hanyar Tsangaya da waɗanda suka haddace ta hanyar Musabaka.

Mun gane cewa babu wata hanya da za ta haɗa su wuri ɗaya don su fahimci juna, su gabatar da takardu da wayar da kai duk da cewa dukkanmu muna da manufa ɗaya da za mu cimma, wato Al-Ƙur’ani ɗaya ne kawai; Annabinmu Muhammad (SAW) ɗaya ne; muna fuskantar Alƙibla ɗaya; muna da littafi ɗaya, al’umma ɗaya; to yaya za mu haɗu?

A cikin ƙungiyarmu, idan muna son shirya wani abu, muna da hanyoyi da yawa na aika saƙonni ga mabiyanmu. Amma muddin akwai haɗin kai, muna son samun haɗin kan al’ummar Musulmi; kuma wannan shi ne mafi muhimmanci. Sarkin zai jagoranci taron. Ya kira mu kuma mun amsa. Muna cikin wannan shirin.

Amma akwai rashin fahimta da yawa game da wannan taron; me ya sa?

’Yan siyasa sun shigo shi ya mutane suna tunanin cewa gwamnati ce ta shirya taron. Ba gaskiya ba ne. Na gaya muku wa ya shirya shi; mu ne, ƙungiyoyin Musulunci.

Ina kuke a lokacin da muka shiga tsakani kan batun Jamhuriyar Nijar da Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS)? Shin ba malaman ba ne suka haɗu suka shiga tsakani kuma zaman lafiya ya samu tsakanin Najeriya da Nijar? Wannan shiga tsakani yana tasiri mai yawa; ya haifar da wayar da kai sosai tsakanin Najeriya da Nijar kuma ya kawo sauyi da yawa.

Don haka, a matsayinmu na malaman Musulunci, muna jin cewa wajibi ne a garemu mu sami wurin da za a cike gibin da ke tsakanin makaranta Al-ƙur’ani da mahaddata ta hanyar Tsangaya da waɗanda suka yi ta hanyar Musabaka kuma suka ƙara koyon Tajweed.

Muna son rufe wannan giɓi don su iya haɗuwa su fahimci juna; kuma a ƙarshe, za a gabatar da takardu.

Yaya kuke shirin tara kuɗin wannan taron?

Al’ummar Musulmi za su iya ɗaukar nauyinsa. Na gaya maka, a ƙarƙashin ƙungiyarmu muna da masallatan Jumu’a sama da 15,000 kuma idan muka ce kowane masallaci ya bayar da gudummawar N10,000, kuna aka  ninka shi sau 15,000, nawa ke nan?

Akwai masu fatan alheri da yawa waɗanda suke son bayar da gudummawa a matsayin domin neman lada saboda Allah. Don haka al’ummar Musulmi na da hanyoyin kawo gudummawa ta hanyar irin wannan taron.

Mutane da yawa sun dage cewa akwai mai ɗaukar nauyi na musamman na taron; me za ka ce?

Babu mai ɗaukar nauyi na musamman na wannan taro. Mutane kawai suna faɗin abin da suke so, amma a yadda muka sani, muna neman gudummawarku. Don Allah ku kawo gudummawarku kuma ni ma zan kawo tawa.

Kuna tsammanin al’ummar Musulmi ba za su iya ɗaukar nauyin irin wannan shirin ba ne? Idan wannan shirin zai ci Naira biliyan daya ko biyu, a ƙarƙashin JIBWIS, a cikin wata guda za mu iya tara har zuwa N600 miliyan ko biliyan ɗaya. Me kuke tunani game da sauran ƙungiyoyi? Ba za su iya yi ba? Idan gwamnati tana son shiga ta bayar da gudummawa, wa zai ce a’a?

Shin mu ba wani ɓangare na gwamnati ba ne? Mu ne muka kawo gwamnati kan karagar mulki, don haka muna da ’yancin mu nemi ta ɗauki nauyi ko ta ba da taimako tunda suna son zaman lafiya da jituwa su mamaye a Najeriya.

Me ya sa wannan taron ke zuwa a lokacin da ake fama da matsanancin ƙunci a ƙasar?

Ai ba a kan ƙunci ba aka shirya ahi, akwai wasu tarurruka da aka gudanar a wannan lokacin. Me ya sa ba za mu iya gudanar da wannan taron ba? Lokacin ƙunci lokaci ne na wayar da kan al’ummar Musulmi don su fahimta. Ƙuncin ya fito daga wa? Daga Allah; kuma idan ka sami kanka cikin jin daɗi, ya fito daga wa? Daga Allah. Don haka, a koma ga Allah. Muna buƙatar ci gaba da karanta Al-ƙur’ani mai girma da kuma yaɗa tauhidi. Kuma idan ka yi imani da Allah, zai yi maka abubuwa da yawa.