Musulmi na fuskantar kalubale a Najariya -Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya cew al’ummar Musulmi na fuskantar kalubale iri daban-daban a kasar nan.Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da kwamitoci 13 da kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa ta kafa domin taimaka mata wajen gudanar da ayyukanta wanda a ka yi a Kaduna. “A tarihin kasar […]

Musulmi na fuskantar kalubale a Najariya -Sarkin Musulmi

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar NasarawaMai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya cew al’ummar Musulmi na fuskantar kalubale iri daban-daban a kasar nan.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da kwamitoci 13 da kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa ta kafa domin taimaka mata wajen gudanar da ayyukanta wanda a ka yi a Kaduna.
“A tarihin kasar nan ba a taba samun lokaci da Addinin Allah da Al’ummar Musulmi suke fuskantar kalubale masu yawa ba sai a wannan lokaci.  Kuma ba mu san dalili ba, wannan ya sa muke ganin dole ne mu mike tsaye mu hada kanmu. Yin hakan zai sa Allah Ya ba mu mafita,” inji Sarkin Musulmin.
Ya kara da cewa “Haka kuma muna sane da cewa Jama’atu Nasril Islam na fama da kalubale masu yawa. Shi ya sa nake ganin taruwarmu a nan ya nuna a shirye muke mu hada kai domin ciyar da wannan kungiya gaba. Jama’atun jiya ba daidai take da Jama’atun yau ba, saboda kalubalen da fuskantar rayuwar Musulmi tun harin 11 ga Satumba da aka kai wa kasar Amurka. Saboda haka ya rage a gare mu, mu Musulmi mu tashi tsaye a kan gaskiya mu kuma rika aiki da koyarwar Alkur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW).”
Sarkin Musulmin ya kuma bukaci malamai su tashi tsaye wajen hada kan jama’arsu, ya ce idan kawunan malamai na rabe ba babu yadda za a yi a samu nasara. Haka kuma Sarkin Musulmin ya nuna bukatar cewa zai fi da cewa idan kungiyoyin Musulmi da ke Kudancin kasar nan suka hada kai da na Arewa.
“Dukkanmu daya muke, sannan zan so ganin ranar da kungiyoyin addinin Musulunci da ke Kudu na gayyatar ’yan uwansu da ke Arewa a duk lokacin da za su yi taro. Yin hakan zai yi matukar taimakawa wajen ciyar da addinin gaba. Baya ga haka ina son Musulmi su sani cewa Jama’atu ba kungiyar Musulmin Arewa ba ce kadai, kungiyace ta Musulmin kasar nan baki daya,” inji shi.
Ya shawarci wakilan kwamitocin da aka kafa su ji tsoron Allah su gudanar da ayyukan da aka dora musu domin ci gaba Musulunci.
A jawabin Babban Sakataren Jama’atu, Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya ce an kafa kwamitocin ne saboda su taimaka wa kungiyar wajen cimma bukatocinta.
A cewarsa, kalubalen da ke fuskantar Musulunci ya zama dole duk wani Musulmi ya ba da gudunmawarsa wajen magance su da kuma ci gaban addinin. Ya ce wasu daga cikin kalubalen sun hada da na fannin ilimi da siyasa da tsaro da sauransu.