Musulmi na rayuwa cikin kunci a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Jama’ar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka na ci gaba da rayuwa a cikin fargaba, musamman ma al’ummar Musulmi inda kungiyar agaji ta Medecin Sans Frontieres ta bayyana cewa kimanin su dubu 7 ne suka fada daji sakamakon wata arangama tsakanin dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka da ’yan kungiyar makiyan Balaka.Arangamar ta faru ne […]
Jama’ar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka na ci gaba da rayuwa a cikin fargaba, musamman ma al’ummar Musulmi inda kungiyar agaji ta Medecin Sans Frontieres ta bayyana cewa kimanin su dubu 7 ne suka fada daji sakamakon wata arangama tsakanin dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka da ’yan kungiyar makiyan Balaka.
Arangamar ta faru ne bayan da ’yan makiyan Balakan suka kai wani hari ga ayarin motocin dakarun Tarayyar Afirka a lokacin da suka raka tawagar wasu musulmi fice wa daga Jamhuriyar Tsakiyar Afrika zuwa kasar Chadi mai makwabtaka da su. Harbe-harben da aka yi tsakanin bangarorin biyu ya haifar da jikkatar mutane uku, kamar yadda kungiyar agaji ta likitoci ta bayyana.
Zuwa yanzu, hukumonin garin Bossangoa da ke yankin Arewa-maso-Yamma sun ce ba Musulmi daya da ya rage a garin. Kafin ficewarsu daga garin dai, ’yan gudun hijirar sun taru ne a wata makarantar Islamiyya da kuma harabar wani coci da ke garin. Sun yi hakan ne kuma saboda tsoron abin da ka iya faruwa idan suka zauna a cikin gidajensu.
A harshen Sango da aka fi amfani da shi a kasar dai, sunan kungiyar ‘Anti-Balaka’ na nufin ’yan taurin da adda ba ta ci, kuma sun ba kungiyar wannan sunan ne saboda ya dace da yadda ’yan kungiyar Seleka ke amfani da adda a matsayin babban makaminta.
Dakaru fiye da 8,000 ke ci gaba da aikin samar da zaman lafiya a kasar, ciki har da 2,000 daga kasar Faransa. Sai kuma saura daga kasashen Afirka. Amma Majalisar dinkin Duniya ta fara wani shiri da zai samar da karin dakaru dubu 12 kafin watan Satumbar bana, wanda za su kunshi sojoji dubu 10 da ’yan sanda dubu 2.