‘Musulmi ne suka fara gano nahiyar Amurka’

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Musulmi ne suka gano nahiyar Amurka fiye da shekara 300 kafin masanin nan dan kasar Italiya, Christopher Columbus ya yi ikirarin gano yankin a shekarar 1492 lokacin da yake bincike don nemo sabuwar hanyar da za ta isa kasar Indiya daga nahiyar Turai. Ya yi bayanin hakan […]

‘Musulmi ne suka fara gano nahiyar Amurka’
‘Musulmi ne suka fara gano nahiyar Amurka’

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Musulmi ne suka gano nahiyar Amurka fiye da shekara 300 kafin masanin nan dan kasar Italiya, Christopher Columbus ya yi ikirarin gano yankin a shekarar 1492 lokacin da yake bincike don nemo sabuwar hanyar da za ta isa kasar Indiya daga nahiyar Turai.

Ya yi bayanin hakan ne lokacin wani taron shugabannin Musulmin Kudancin nahiyar Amurka da ya gudana a Istanbul, babban birnin kasar Turkiyya, inda ya nuna wani kundin adana bayanai wanda Mista Columbus ya ambaci wani masallaci da ya iske akan wani tsauni da ke kasar Cuba. Kuma Mista Erdogan din ya ce Musulmai suka fara isa nahiyar a cikin shekarar 1178.
Shugaban Turkiyyar wanda kuma shi ne shugaban jam’iyya mai mulki ta AK Party ta samo tushe ne daga siyasar addinin Islama. Sai dai kuma shugaban bai ba da hujjojin da za su tabbatar da hakan ba, amma ya ce alaka tsakanin Kudancin Amurka da addinin Islama ta fara ne daga karni na 12.
Kodayake, a wata makala da aka wallafa a shekarar 1996, wani masanin tarihi Youssef Mroueh ya ce labarin gano nahiyar da Mista Columbus ya bayar ya tabbatar da cewa Musulmi ne suka fara isa nahiyar da kuma cewa addinin ya yadu a gaba a duniya baki daya.
Har ila yau, yawancin masana sun yi amannar cewa batun ba haka ba ne, inda suka bayyana abin da aka gani a tsaunin da wani abu da ya ti kama da masallaci.