Musulmi su ne matsalar kansu – Dokta Gumi
Sanannen malamin addinin Musulunci nan Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya ce Musulmi su ne matsalar kansu da kansu ba wani ba a kasar nan, domin duk inda aka kashe Musulmi a yankin Arewa maso Gabas indan aka bibiya sai a ga Musulmi dan uwansa ne ya kashe shi. Dokta Ahmad Gumi ya bayyana haka ne […]
Sanannen malamin addinin Musulunci nan Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya ce Musulmi su ne matsalar kansu da kansu ba wani ba a kasar nan, domin duk inda aka kashe Musulmi a yankin Arewa maso Gabas indan aka bibiya sai a ga Musulmi dan uwansa ne ya kashe shi.
Dokta Ahmad Gumi ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ya fito daga bitar watan Ramadan da Majalisar koli ta Shari’ar Musulunci ta shirya a Kaduna.
Malamin ya ce hanyar fita daga wannan matsala da Musulmi suka jefa kansu a ciki ita ce su tashi su nemi ilimi. “Musulmi ne matsalar kansu a kasar nan a yau. Idan ka ji an ce an kashe Musulmi a Maiduguri da zarar ka bincika sai ka ji Musulmi ne dan uwansa ya kashe shi. Saboda haka ilimi shi ne zai kawo karshen wannan matsala, saboda yawancin al’umma na fama da rashin ilimi. Amma idan aka mayar da hankali wajen bai wa jama’a ilimi sai a magance matsalar,” inji shi.
Dokta Gumi ya kuma shawarci ’yan Najeriya su yi wa shugabannin da aka zaba addu’ar samun nasara a mulkinsu, kuma su kara yi wa gwamnatin nan hakuri ta zauna da gindinta domin yi wa ’yan kasa aiki.
Sheihin Malamin ya nemi Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wajen hada kan ’yan kasa maimakon ’yan jam’iyya, kuma akwai bukatar ta cika alkawarin da ta yi wa jama’a a lokacin yakin neman zabe.
Tun farko a jawabinsa mai taken: “Bukatar Sauyi da kalubalensa ga Al’ummah,” a wajen taron, Shugaban Majalisar, Dokta Ibrahim Datti Ahmad ya bayyana cewa sojoji kadai ba za su iya kawo karshe ’yan Boko Haram ba a kasar nan.
Ya ce, a yayin da ake ci gaba da amfani da soja wajen yakar ’ya’yan kungiyar, a daya gefen ya kamata a fara tattauna da su.
Ya ce “Matsalar tsaro musamman Boko Haram matsala ce da ke bukatar barazana da lallashi, wato a yi amfani da karfin soja (abin da aka makara) a daya gefen kuma a tattauna da ’yan kungiyar. Tarihi ya nuna babu wata tada kayar-baya ta kowace irin manufa da aka taba magancewa ta hanyar karfin soja kawai. kungiyoyin Taliban da ’yan tawayen FARC a Afghanistan da Columbia sun isa misali. Kuma wajibi ne a yi gaggawar samar da wani tsari na tallafi da sake gina mutanen da suka jikkata a Arewa maso Gabas don su samu su farfado.”
Dokta Ahmad ya ce gwamnati mai ci ta zauna da shirin yiwuwar samun bore daga tsagerun Neja-Delta da barazanar raba kasa daga mutanen Kudu maso Gabas saboda rasa tasiri a sabon zubin siyasa a yanzu.
Sai ya ja hankalin gwamnatoci su tashi tsaye wajen magance bakin talauci da rashin aikin yi da suka addabi jama’ar kasar nan, musamman matsalar wutar lantarki wadda za ta taimaka wajen kawar da talauci da rashin aiki.
Ya kuma nemi malamai su yi amfani da watan Ramadan wajen yi wa jama’a bayani tare da taimaka wa gwamnatoci wajen rage kaifin bukatun jama’a. “Ina kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya su yi amfani da ofishohin Mataimakin Shugaban kasa da na mataimakan gwamnoni Kiristoci don sanya malaman Kirista irin wannan aiki,” inji shi.
Ya nemi a yi hattara domin kauce wa makiya da ka iya neman kawo karshen hadin kan da aka samu tsakanin Arewa da Kudu maso Yamma don tabbatar da dinkewar kasar nan da ci gabanta.