Musulmi suka fi cutuwa da Boko Haram a Najeriya – Farfesa Bunza
Shin mece ce manufar ’yan Boko Haram, ta yaya suka fara kuma ta yaya suke gudanar da al’amuransu, me ake ciki a yanzu dangane da wannan rikici da ya ki ci kuma ya ki cinyewa? Wadanne hanyoyi ya kamata a bi domin hana aukuwar irin wadannan rikice-rikice masu nasaba da addini a nan gaba a […]
Farfesa Mukhtar Bunza, a lokacin da yake gabatar da makalarsa a wajen taron
Shin mece ce manufar ’yan Boko Haram, ta yaya suka fara kuma ta yaya suke gudanar da al’amuransu, me ake ciki a yanzu dangane da wannan rikici da ya ki ci kuma ya ki cinyewa? Wadanne hanyoyi ya kamata a bi domin hana aukuwar irin wadannan rikice-rikice masu nasaba da addini a nan gaba a Najeriya? Aminiya ta tattauna da masani Farfesa Mukhtar Umar Bunza, malami a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, wanda ya kasance babban bako mai jawabi a wajen taron kasa da kasa dangane da tsaro da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, a makon da ya gabata.
A bincikenka mene ne asalin Boko Haram kuma mece ce manufarsu?
A nan zan iya cewa babu tabbatacciyar amsa game da asalin Boko Haram sai dai ban sani ba ko nan gaba idan an ci gaba da bincike a kan hakan. A yanzu dai bayanan da muke da su a kan hakan suna da dama. Yayin da wasu ke ganin Boko Haram sun samo asali ne daga Salafi/Sunni na kasar Saudiyya. Wasu na ganin cewa gyauron Maitatisne ne ko Kalakato ko kuma Shi’a, musaman ma idan aka yi duba da irin akidarsu ta juya baya ga ilimin zamani (Boko). Har ila yau wasu suna da ra’ayin cewa wadannan ’yan tayar da kayar baya sun samo asali ne daga Jihadin Shehu Usman Danfodiyo da sauransu. Sai dai ko ma mene ne asalinsu ya kamata a sake duba batun da ake yi na danganta Boko Haram da Musulunci, kasancewar Musulunci bai tsaya kan kare jinin Musulmi kadai ba, yana kokarin kare Kiristoci da Yahudawa.
Shin ko a wane matsayi za a dauki ’yan Boko Haram?
Ba daidai ba ne daukar da ake yi wa ’yan Boko Haram a matsayin cikakkun Musulmi masu bin sunnar Manzon Allah saboda kawai don suna kiran kansu da kungiyar ‘Jama’atu Ahlissuna lidda’awati waljihad.’ Mun san cewa duk wanda yake son samun karbuwa a wajen jama’a yana kokari ya hada kansa da wani abu da ya shafi tabbatar da adalci da sauransu.
Idan kana so ka gane haka sai ka gane hakan sai ka auna ka ga shin aikinsu ya dace da koyarwar Sunna? Domin a Musulunce, ana hukunci ne da aiki ba wai abin da yake fitowa daga baki ba. Kuma tarihi ya nuna irin yadda Manzon Allah ya yi hulda da al’ummarsa ba tare da nuna kyama ga makiyansa ba. Shin wadannan ’yan tayar da kayar baya da ke fakewa da sunan Musulunci hakan suke ko a’a? Kuma babu wani dalili da zai sa don ba ku bin ra’ayi daya da sauran Musulmi ’yan uwanku, ku nuna kyama a gare su ta hanyar kai musu hare-hare. Ina so a fahimci cewa ba wai a Addinin Musulunci ne muke da rabe-raben ra’ayoyi ba, domin a Kiristanci ma akwai hakan. Za ka samu irinsu Katolika da sauransu amma hakan ba ya nufin wani bangare ya rika kallon daya bangaren a matsayin makiyi, ballantana har ya abka masa.
Shin me ya jawo wadannan rikice-rikice da ke da nasaba da ’yan Boko Haram?
Wani dalilin da masu bincike suke ganin shi ne ya jawo tashin rikicin Boko Haram a Jihar Borno, shi ne kasancewar Musulunci daga wuraren ya zo kasar nan a karni na 9 da 10. Sai dai ba kamar a Sakkwato ba, inda aka mayar da hankali wajen koyon ilimin addini iri daban-daban amma a Borno an mayar da hankali ne ga koyon karatun Alkur’ani da kuma haddarsa, inda aka yi watsi da neman sauran fannonin ilimi da suka shafi addinin. Hakan ya sa aka sami “malamai ba masu cikakken ilimi ba” wadanda kuma za a iya jan ra’ayinsu cikin sauki.
A ganinka me ya jawo rikicin nan na Boko Haram ya dauki tsawon lokaci ba a shawo kansa ba?
Zan iya cewa rashin daukar al’amarin da muhimmanci da gwamnati ta yi a farkon tashin rikicin, domin zan iya tunawa sai da aka dauki kwanaki 8 kafin Gwamnatin Tarayya ta wancan zamanin, kafin ta amince cewa ’yan matan Chibok sun bata. A wancan lokaci da farko tunanin da ake yi ai abu ne da ya shafi Musulmi ko ’yan Arewa, domin tunaninsu shi ne Musulmi ’yan Arewa ne suka kitsa al’amrin domin Shugaban Kasa na wancan lokaci Goodluck Jonathan ya kasa mulkar kasar; lamarin da ya sa ’yan Kudancin kasar nan suka dauke shi a matsyain wata hanya ta ‘juyin mulki.’
Sai dai wannan shaci-fadi ne, domin idan aka yi la’akari da yanayin hare-haren da ’yan Boko Haram suka rika kaiwa a kan mutane daban-daban, zai yi wuya mutum ya ce ga wani rukuni da suka nufa da hare-harensu. Da farko idan mun duba, sun fara kai hare-harensu kan jami’an tsaro, daga baya kuma suka koma kan kowane rukuni na al’umma; hatta mata da kananan yara ma ba a bar su a baya ba. Haka kuma rikicin Boko Haram ya taba dukkanin addinai guda biyu, Musulunci da Kiristanci. Za mu iya cewa bisa kididiga da bayanai da muke da su, addinin Musulunci da ’ya’yan kungiyar suke da’awar suna karewa ya fi shan wahala a wannan lokaci, domin an sami akalla hare-hare 37 da aka kai masallatai, yayin da aka sami hare-hare 12 kadai da aka kai coci-coci.
Wadanne hanyoyi kake ganin za a bi wajen kauce wa sake faruwar irin wannan rikici a nan gaba?
Wajibi ne gwamnati ta samar da aikin yi ga matasan kasar nan don a rage yawaitar shigarsu cikin al’amurra aikata laifi cikin sauki. Kamar yadda bincike ya nuna, talauci ya taka muhimmiyar rawa wajen iza wutar rikicin, inda aka rika amfani da yanayin tattalin arzikin kasar aka ja ra’ayin mutanen da ke wa da talauci a kan dan abin da bai kai ya kawo ba.
Har ila yau akwai bukatar a samar da isassu kuma ingantattun kayan aiki ga jami’an tsaro tare da kara kulawa da su ta hanyar gyara musu albashi tare da kula da duk wani abu da ya shafi walwalarsu. Hakan zai sa su samu natsuwa tare da kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Haka kuma dole gwamati ta yi kokarin gano ta yadda ’yan Boko Haram suke samun kudi da makamai da kuma kokarin gano ko da sa hannun kungiyoyin kasashen waje a cikin wannan rikici. Akwai bukatar a dauki wasu jami’an tsaro masu kwarewa tare da horar da wadanda ke aiki a yanzu a fadin kasar nan, kasancewar akwai ’yar gazawa a wajen tafiyar da rikicin Boko Haram daga jami’an tsaro. Don haka akwai bukatar a yi gyara a wannan fannin. A bincikenmu, mun gano cewa su kansu jami’an tsaron da muke da su a kasar nan sun yi wa kasar kadan, don haka akwai bukatar a dauki sabbi don matsalolin Najeriya suna da yawa.
Haka kuma akwai bukatar a samar da sabbin makamai ga jami’an tsaro, kasancewar wadanda suke a hannunsu a yanzu tsofaffi ne, wadanda suka dade ana amfani da su. Har ila yau gwamnati ta rika daukar matakin gaggawa a kan abin da ya shafi tsaro a kan lokaci a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Gwamnati ta yi kokarin hukunta wadanda aka samu da hannu a cikin aikata laifukan rikicin Boko Haram, don haka ya zama izna ga na baya. Kuma akwai bukatar a shigar da shugabannin gargajiya da suka hada da sarakuna da masu unguwanni cikin sha’anin da ya shafi sulhunta rigingimu da rikice-rikice. A mafi yawan lokuta talakawa sun fi ganin kima tare da jin maganar sarakunan da ke kusa da su fiye da na ’yan siyasa da jami’an tsaron da suka yi suna wajen cin hanci da rashawa.
Iyaye su ma ba a bar su a baya ba, suna da rawar takawa wajen sanya idanu a kan ’ya’yansu da bibiyar halin da suke ciki tare da kokarin sauya tunanin ’ya’yansu, wadanda suka riga suka shiga cikin rikicin. Na ji dadin maganar da mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi a kan a samar da hukuma da za ta rika kula da masu wa’azi.
Kasancewar duk abin da aka bari kara zube babu tsari, to za a iya samun wasu su fake da hakan, su rika batanci wanda kuma kafin a shawo kan lamarin za a sha wuya. Yayin da aka ga mutum ya fara da’awa, ana jin zai kawo matsala ta addini ko ga zaman lafiya. Idan aka sami hakan
za a yi saurin dakatar da shi.
A ganinka, ko zuwa yanzu kana ganin an samu nasarar kawo karshen wannan rikici na Boko Haram?
Zan iya cewa ko ba a kawo karshensa a yanzu ba, to babu
shakka an sami nasarar dakile rikicin, duba da saukin kai hare-haren da aka samu. Ko shi kansa samun halin gudanar da wannan taro da muke yi a yanzu yana daya daga ciki, domin na san a baya, jami’o’i da kwalejojin ilimi sun sha tunani tare da kokarin shirya makamancin wannan taron amma abin bai yiwu ba saboda matsalar a wannan lokaci kowa tsoro yake ji a ce ma za a sa sunansa a cikin masu shirya taron don gudun daukar fansa daga ’yan tada kayar bayan. A wannan lokacin ma yadda za a samar da tsaro a wurin da za a yi taron aiki ne domin za a iya wayar gari an sanya bam a wurin.
A nan ya zama dole mu yaba kokarin wannan gwamnatin, karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, saboda irin jajircewa da ya yi wajen ganin an kawo karshen wannan rikici, wanda kuma kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.