Musulmi sun bukaci a ba su masarauta a Kachia … Ba a sarakuna biyu a gari daya – kabilun Kachia

Al’ummar Musulmin garin Kachia sun bukaci gwamnatin Jihar Kaduna ta kirkiro musu da masarauta daga masarautar Adara da ke jihar domin kare sake aukuwar rikici mai alaka da addini da aka yi a yankin kwanakin baya wanda ya yi sandiyyar rasuwar mutane da dama.A cewar al’ummar Musulmin suna ganin kirkiro musu da masarautar za ta […]

Musulmi sun bukaci a ba su masarauta a Kachia … Ba a sarakuna biyu a gari daya – kabilun Kachia
Musulmi sun bukaci a ba su masarauta a Kachia … Ba a sarakuna biyu a gari daya – kabilun Kachia

Al’ummar Musulmin garin Kachia sun bukaci gwamnatin Jihar Kaduna ta kirkiro musu da masarauta daga masarautar Adara da ke jihar domin kare sake aukuwar rikici mai alaka da addini da aka yi a yankin kwanakin baya wanda ya yi sandiyyar rasuwar mutane da dama.
A cewar al’ummar Musulmin suna ganin kirkiro musu da masarautar za ta taimaka wajen kawo karshen rikici da ke tashi a garin na Kachia a tsakanin Musulmi da Kiristocin yankin.
Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban al’ummar Musulmin Kachia, Malam Idris Sulaiman ya ce samar da masarautar zai kare martaba da al’adun Musulmin yankin wanda hakan kuma zai samar da zaman lafiya a yankin.
“kirkiro mana da masarauta daga cikin masarautar Adara a Kachia zai taimaka wajen kawo karshen yawan rikicin addini da kabilanci da ke neman kunno kai a garin Kachia. Saboda haka muke ganin idan aka kirkiro mana da masarauta za ta kare mana mutunci da al’adunmu a yankin,” inji shi.
Al’ummar Musulmin sun kuma nuna bacin ransu game da kwamitin da Shugaban karamar Hukumar Kachia ya kafa domin samar da maslaha ga rikicin da aka yi a yankin inda suka yi zargin cewa ’yan kwamitin akasarinsu ba Musulmi ba ne saboda a cewarsu Musulmi hudu ne kawai a ciki.
Don haka sai suka bukaci da gwamnatin jihar ta kafa nata kwamitin binciken domin kawo karshen matsalar da ke neman tashi a karamar hukumar.
A martanin shugabannin kungiyoyin kabilun da ke Kachia sun yi watsi da kiraye-kirayen kirkiro da masarauta a yankin inda suka ce wannan ba zai maido da zaman lafiya ba a yankin.
Shugaban kungiyar Ci-gaban kabilun Adara wanda ya jagoranci kungiyoyin kabilun yankin zuwa taron manema labarai, Peter Gulbee ya ce babu yadda za a yi a samu sarakuna biyu a gari daya.
“Ba a taba yi ba, a ce wai an kirkiro masarauta daga cikin hedikwatar wata masarauta a gari daya. Saboda haka muke ganin ba zai yiwu a kirkiro masarauta ba a Kachia. Amma akwai bukatar a zauna domin a tattauna matsalolin da ke faruwa a yankin da nufin samar da maslaha,” inji shi.
Ya ce har yanzu ba su san ainihin mai wannan fili na Idi da ake rigima a kai ba. Kuma ya musanta zargin da Musulmi ke yi cewa akasarin mutanen da shugaban karamar hukumar ya nada a cikin kwamitinsa don binciken musabbabin rikicin na kwanakin baya Kiristoci ne. Ya ce akalla akwai mutum shida da ya san Musulmi a cikin kwamitin mai mutum 24.
Mista Gulbee ya ce Musulmi da Kiristocin Kachia sun dade suna zaune lafiya da junansu kafin rikicin ya auku, saboda haka ya bukaci shugabannin Jama’atul Nasril Islam da na kungiyar Kiristoci (CAN) a yankin su zauna teburin sulhu domin kawo karshen rikicin da ke neman tashi a yankin wanda tashinsa ba zai yi wa kowa dadi ba.