Musulmi sun yi sallah a Coci a Kaduna
Musulmi sun yi sallar jana’iza a cikin wani coci da ke garin Kaduna domin tabbatar da cewa a tsakanin musulmi da kirista akwai fahimtar juna. Wannan al’amarin ya faru ne a Unguwar Rimi da ke Kaduna kan titin Lema Jibrilu (tsohon titin Kinshasha). A wannan wurin akwai masallaci da aka fi sani da suna “Masallacin […]

Musulmi sun yi sallar jana’iza a cikin wani coci da ke garin Kaduna domin tabbatar da cewa a tsakanin musulmi da kirista akwai fahimtar juna.
Wannan al’amarin ya faru ne a Unguwar Rimi da ke Kaduna kan titin Lema Jibrilu (tsohon titin Kinshasha). A wannan wurin akwai masallaci da aka fi sani da suna “Masallacin Sheik Imam Daniyalu Shitta” da kuma “Cocin Nasara Baptist” (wanda aka fi sani da Bakin Coci) da suke makwabtaka, don katanga ne kawai ya raba su shekaru kusan arba’in, kuma duk da rikicen-rikicen da suka addabi garin Kaduna a baya babu wanda ya kai wa wani hari.
Rabaran Silas Shaba shi ne shugaban Cocin Nasara Baptist, ya bayyana cewa, “Ni dan asalin garin Paiko ne da ke jihar Nija, a iyalinmu akwai muslmi da kuma kirista. Bayan na kammala firamare sai na wuce Makarantar Horar da Pastoci (Nigerian Baptist Theological Seminary) da ke Unguwar Hayin Banki Kaduna, inda na kammala a shekarar 1980. An tura ni garin Magama wacce ake kira da suna Rijau a yanzu, a shekarar 1985, sannan aka maido ni Kaduna. Na yi ritaya watanni biyu da suka wuce, sai dai ina kula da cocin kafin mai karbana ya iso. Akwai musulmi da kiristoci a iyalinmu, don haka in sun zo wurina a Kaduna sai in kai su wajen Alhaji Ibrahim Oloyede Sulaiman don su rika sallah a masallacin da ke makwabtaka da Cocinmu. Ina halartar gidan Alhaji don biki ko abin juyayi , shi ma yana halartar nawa. Wannan ya sa muka kara shakuwa da juna muna zaune lafiya.”
Rabarab ya ce “Don babu addinin da za a gudanar idan babu zaman lafiya. Don littafin Zabura aya ta 24 ya ce “kasa na Allah ne”. Duk rigiggimun da ke faruwa a Najeriya laifin ‘yan siyasa ne. Idan sun ci zabe sai su bar mu talakawa cikin wahala, su kuma suna can suna sharholiyarsu da iyalansu da ‘yaya’nsu.”
Game da yadda aka yi musulmi suka yi sallah a cocinsu kuwa sai ya ce, “ lokacin bikin ‘yata ‘yar uwarta musulma ta zo Kaduna, amma sai Allah Ya yi mata rasuwa. Sai na je gidan Alhaji Ibrahim Sulaiman na fada masa abin da ya faru, na ce ina son musulmi su zo su yi mata Sallah su birne ta.”
Nan da nan Alhaji ya gaya wa makwabta na titin da ke Unguwar Rimi, aka yi mata wanka, aka ce za a yi mata sallah a cocin, don yana da girman da zai dauke mutane, saboda masallacin karami ne. Rabaran ya ce a yi mata, duk da dai wadansu musulmi da wadansu kirista suna ganin bai dace ba.
Rabaran ya ce yin Sallah a Coci ba laifi ba ne, don duk bauta wa Allah kowa yake, sai dai ta hanyoyi daban-daban. Sai aka yi mata Sallah, sannan aka dauke ta aka je makabartar musulmi aka binne ta.
Rabaran ya kara da cewa, akwai wani mai motar haya musulmi da ya kawo kaya Coci, ana sauke kaya sai lokacin sallah ya yi. Sai ya ce ko zai iya yin sallah a Cocin? Sai wadansu suka ce a’a. Da Rabaran ya ji sai ya ce yana iya yin sallarsa, domin ai ba laifi bane.
Limamin masallacin Sheik Imam Daniyalu Shitta, Alhaji Ibrahim Oladejo Sulaiman, ya ce masallacinsu da kuma cocin suna makwabtaka da juna na tsawon lokaci ba tare da wata matsala ba.
Wani wakilin Jama’atul Nasril Islam (JNI) daga Jos ya ce Firimiyan jihar Arewa Sa Ahmadu Bello yana sallah a masallacin titin Kano da ke cikin garin Kaduna kuma Katanga ta raba shi da coci. Ya kara da cewa, akwai kuma masallaci da Coci a Jos inda katanka ta raba su a titin Adebayo, masallacin an sanya masa suna Nurudeen, amma an fi saninsa da suna “Masallacin ‘Yan biyu.” Cocin kuma ana kiransa da suna “Cocin ‘Yan biyu.”
Dalilin hakan sh ine, wani bayarabe ne ya nemi a ba shi filin da zai gina Cocin a Jos, da aka ba shi izini sai ya ce ga kaninsa yana son filin gina masallaci don shi musulmi ne. Sai aka ce ya rubuta kuma aka ba shi izini, aka gina masallaci kuma ana zaman lafiya.
Alhaji Ibrahim Sulaiman ya ce, “Da Rabaran ya yi ritaya sai aka turo wani rabaran na yanzu, watau Rabaran Silas Shaba, wandashi ma muke zumunci sosai. Don ina zuwa wurinsa a Coci, shi kuma yana zuwa wurina don bikin aure ko suna. Sannan idan ‘yan uwansa musulmi sun zo sai ya kawo su wurina su yi sallah, mu yi ta hira.”