Musulmi sun yi taro kan zaman lafiya a Kamaru

Kusan daukacin limaman addinin Musulunci na kusurwa hudu da ke kasar Kamaru sun halarci taron da ya hada kawunansu domin su tattauna matsalolin da jama’a suke fuskanta wurin tafiyar da addininsu da kuma neman sanin hanyoyin da za su bi domin fadakar da jama’a a cikin irin hudubobin da za su yi a sallar jumma’a.  […]

Musulmi sun yi taro kan zaman lafiya a Kamaru
Musulmi sun yi taro kan zaman lafiya a Kamaru

Kusan daukacin limaman addinin Musulunci na kusurwa hudu da ke kasar Kamaru sun halarci taron da ya hada kawunansu domin su tattauna matsalolin da jama’a suke fuskanta wurin tafiyar da addininsu da kuma neman sanin hanyoyin da za su bi domin fadakar da jama’a a cikin irin hudubobin da za su yi a sallar jumma’a. 

Sai dai kuma a wannan karon wannan taron ya zo ne a lokacin da Kamaru take fuskantar matsalar rashin tsaro masamman ma ta yankin arewacin kasar, inda ’yan kungiyar Boko Haram suke rubanya kai hare-hare. Haka nan kuma ta yankin gabashinta inda anan farmakin da wasu masu mayakan sa-kai da ake kira ‘anti-Balaka’ suke kai wa Musulmai a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, wannan ya sa a yanzu Kamaru ta cika makil da ‘yan gudun hijiran kasar, saboda haka taken wannan taro wanda aka yi a karo na uku yake: “Tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro a Kamaru, tasirinsa, kalubale da kuma nauyin da ya rataya akan kowane mai fada a ji”.
Sakamakon tashin hankali a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya sa a yanzu haka sama da mutum miliyan biyu da rabi daga cikin daukacin al’umman kasar na bukatar agaji a dalilin rashin tsaron da ya bazu a cikin kasarsu. Har ila yau, akwai wasu kungiyoyin ’yan tawaye da suke yin kutse lokaci-lokaci a cikin Kamaru da yunkurin neman tayar da tarzoma masamman ma a wasu garuruwan kan iyakarta da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka inda kodayaushe jama’a suke rayuwa akan hatsari. Wadanda suka hada da yin garkuwa da jama’a. A dalilin haka ne, Majalisar limamai da kuma wasu masu fada a ji a fannin addini Musulunci a Kamaru ta tashi domin ta bayar da nata gudunmawar baya ga Gwamnati da kuma sauran shugabannin sauran addinai kamar na Kirista. A dalilin haka ne taro na Majalisar limaman ya mayar da hankali akan addu’o’i, wa’azi, da kuma laccoci wadanda suka danganci batutuwan tabbatar da zaman lafiya, da tsaro.
Har ila yau, jami’an ma’aikatar kiwon lafiya sun fadakar da limamai game da cutar Ebola masamman ma akan matakan neman kariya da suka wajaba a bi. Hakazalika, ma’aikatar kare iyali da kuma ci gaban mata ta fadakar da limamai da sarakunan gargajiya da su nuna wa iyayen yara muhimmancin neman ilimi. A takaice dai wannan taron ya nunar da cewa, yadda akidar addinin kungiyar Boko Haram yake da kuma suke ikirari, ba haka batun yake ba. “Musulunci addini ne da kodayaushe yake neman tabbatar da zaman lafiya, yaki da jahilci, nuna tausayi da kuma fahimtar juna. Don haka taron Majalisar Limamai ya yi kira ga jama’a da kada a yi amfani da addini wurin gallaza wa jama’a, kada a yi amfani da addini domin tayar da tarzoma, da janyo gaba, da kyamar juna a tsakanin al’umomi,” inji shugaban taron.