Musulmi ya shafe shekaru yana limancin dakin ibadar Hindu

Wani Musulmi a kasar Indiya ya shafe tsawon shekaru yana limancin addinin Hindu, a wata karkarar da ke tsakiyar gundumar Bihar Arwal. Tsohon mai suna Sadikue Miyan mai shekara 85, kan tayar da mabiya addinin Hindu da ke kauyen Bihar kowace safiya, ta hanyar kada karararwa da ke rataye a dakin ibadarsu., ta yadda da […]

Musulmi ya shafe shekaru yana limancin dakin ibadar Hindu

Wani Musulmi a kasar Indiya ya shafe tsawon shekaru yana limancin addinin Hindu, a wata karkarar da ke tsakiyar gundumar Bihar Arwal. Tsohon mai suna Sadikue Miyan mai shekara 85, kan tayar da mabiya addinin Hindu da ke kauyen Bihar kowace safiya, ta hanyar kada karararwa da ke rataye a dakin ibadarsu., ta yadda da sun ji karar sai su farka su halarto wajen bautarsu. Wannan lamari dai bai zame musu abin mamaki ba. Abin mamakin kawai shi ne Musulmi ne ke kada wannan kararrawa, inda aikinsa ya zama kwatankwacin na limamin addinin hindu.

“daukacin addinai sun daidaita a bigire daya,” inji Miyan. “Suna koyarwa ne kan kauna da hidima ga al’umma.”

Tsohomn dan shekara 80 ya yi fatan cewa idan ya mutu yana da buri guda: “Ina son a a kai gawata zuwa kogin Ganges.”

Wannan musulmi tun lokaci da yake karatu ya yi kokarin nakaltar harsunan Hindi da Urdu da Larabci, a lokacin yana aji uku na sakandare.

“Bai kamata a tursasa addini ga kowa ba, a bar mutane su zabi addininsu.

Sai dai ba shi kadai ne ke da irin wannan manufa ba, wajen kafa wata sabuwar al’umma da ta ginu kan ’yan uwantaka ba.

Musulmin da ke kauyen Bihar sun bude sabon babi na kyautata zamantakewar lumana da taimakon juna, musamman kan yadda suka sarayar da lokutansu da kudinsu wajen gyara tsohon dakin ibadar addinin Hindu, a bangaren masu bautar Hanuman.

Sannan a lokacin dakin ibadar ba shi da isasshen wuri, al’amarin da ke tursasa wa mabiya addinin gwamuwa a lokautan gudanar da muhimman bukukuwan addini

Ba da dadewa ba, mutanen kauyen suka tsara ayyukan gyaran dakin ibadar, amma sai matsalar fadin wajen ta kawo musu cikas. Lokacin da Musulmin kauyen suka samu labari, sai suka yi hanzari wajen tallafa musu,inda suka bayar da filinsudon fadada dakin ibadar. Kuma sun bayar da gudunmuwar kudi.