Musulmi za su kai rubu’in duniya nan da shekarar 2030
Wani sabon rahoto ya ce yawan Musulmi a duniya zai karu da ninki biyu fiye da mabiya sauran addinai nan da shekara 20 masu zuwa. Sabon rahoton ya yi hasashen Musulmi za su kai rubu’in al’ummar duniya a lokacin. Masu nazari da binciken sun yi amfani da yawan haihuwa da yawan gudun hijira, wajen yi […]
Wani sabon rahoto ya ce yawan Musulmi a duniya zai karu da ninki biyu fiye da mabiya sauran addinai nan da shekara 20 masu zuwa. Sabon rahoton ya yi hasashen Musulmi za su kai rubu’in al’ummar duniya a lokacin.
Masu nazari da binciken sun yi amfani da yawan haihuwa da yawan gudun hijira, wajen yi wannan hasashe, kamar yadda cibiyar bincike ta Pew Forum on Religion and Public Life ta bayyana, inda ta yi hasashen karuwar Musulmi da kashi 1.5 a duk shekara nan da shekara 20, yayin da wadanda ba Musulmi ba za su rika karuwa da kashi 0.7 a duk shekara.
Nazarin mai suna “Makomar Yawan Musulmi a duniya,” ya yi hasashen cewa a shekarar 2030, Musulmi za su kai kashi 26 da digo 4 na al’ummar duniya da aka kiyasta za su kai mutum biliyan takwas da miliyan 217 a wancan lokaci
Hasashen ya ce mutum shida daga cikin 10 na Musulmin za su kasance ne a yankin Asiya da Pacific a shekarar 2030, kuma kasar Pakistan wadda take samun masu kishin Musulunci a baya-bayan nan za ta doke kasar Indonusiya a matsayin kasa mafi yawan Musulmi a duniya.
A Nahiyar Afirka yawan Musulmin da suke Najeriya za su fi na kasar Masar nan da shekara 20 inji rahoton, yayin da karuwar Musulmi a Turai za ta ninka sau uku nan da shekara 20 daga Musulmi miliyan 44 da dubu 100 ko kashi shida cikin 100 na mazaunan yanki a shekarar 2010, zuwa Musulmi miliyan 58 da dubu 200, wato kashi takwas na daukacin mutanen Turai a shekarar 2030.
Rahoton ya ce wasu kasashen Tarayya Turai za su samu karuwar Musulmi ninkin da suke da shi nan da shekarar 2030, inda yawan Musulmin kasar Belgium zai tashi daga kashi shida cikin 100 zuwa kashi 10 da digo 2, sai Faransa da ake sa ran Musulmin su karu zuwa kashi 10 da digo 3 daga kashi bakwai da rabi a yanzu.
Sauran su ne Sweden, kashi 10, maimakon kashi biyar a yanzu, sai Birtaniya da za su karu zuwa kashi 8 da digo 2 maimakon kashi 4 da digo 6. Sai Austria kashi 9 da digo 3 daga kashi shida a yanzu.
Rasha wadda ba ta cikin Tarayyar Turai za ta ci gaba da kasancewa mafi yawan Musulmi a Turai, inda zuwa shekarar 2030 Musulmin za su kai miliyan 18 da dubu 600 ko kashi 14 da digo 4 na mutanen kasar, yayin da a Amurka, Musulmin za su kai kashi daya da digo 7, maimakon kasa da kashi daya da suke da shi a yanzu, lamarin da zai sa su yi kankakan da Yahudawa a yawa a Amurka.