Musulmin garin Wukari sun koka kan gallaza musu

Al’ummar Musulmi yankin Wukari a Jihar Taraba sun koka kan yadda ake gallaza masu tare da yin musu kisan gilla da kwace masu dukiyoyinsu.Koken na al’ummar Musulmin yankin Wukari na kunshe ne a cikin wata takarda da suka fitar dauke da sa hannun Shugaba da Sakataren kungiyar Al’ummar Musulmin garin Wukari Alhaji Ja’afar danbaba da […]

Musulmin garin Wukari sun koka kan gallaza musu
Musulmin garin Wukari sun koka kan gallaza musu

Al’ummar Musulmi yankin Wukari a Jihar Taraba sun koka kan yadda ake gallaza masu tare da yin musu kisan gilla da kwace masu dukiyoyinsu.
Koken na al’ummar Musulmin yankin Wukari na kunshe ne a cikin wata takarda da suka fitar dauke da sa hannun Shugaba da Sakataren kungiyar Al’ummar Musulmin garin Wukari Alhaji Ja’afar danbaba da Malam Sani Sule Sale, wadanda suka bayyana cewa wadanda ba Musulmi ba suna hallaka Musulmi tare da kwace musu dukiyoyinsu a yankin.
Sun ce Musulmin da suka yi kokarin tayar da ginin tamfurare a gidajensu da aka kone wadanda ba Musulmi sun sake bi suna rushewa, kuma ana kashe duk wani Musulmi da ya yi kokarin zuwa gonarsa don yin noma.
Sun ce kazalika wadanda suka yi kokarin yin tafiya a yankin ana hallaka su, kuma jami’an tsaro ba sa daukar wani mataki don hukunta wadanda ke da hannu a wannan aika-aika. “Mun sha kai rahoton yadda ake kashe al’ummarmu ga jami’an tsaro, amma ba wani mataki da aka dauka don kare mu,” inji sanarwar.
Al’ummar Musulmin sun ce an dauke su tamkar ba ’yan kasa ba domin da karfi wadanda ba Musulmi ba ke kwace musu gonaki da filaye da gidajensu amma hukuma ta ki daukar mataki balle ta hukunta wadanda ke yi musu zalunci.
Al’ummar Musulmin wadanda suka nuna goyon bayansu ga shirin maido da zaman lafiya a yankin da Gwamnan Jihar Darius Ishaku yake yi, sun ce wadanda ba sa kaunar zaman lafiya a yankin na yi wa yunkurin da Musulmin yankin ke yi na kawo zaman lafiya kafar ungulu.
Sun bukaci gwamnatin jihar ta kafa wani kwamitin sulhutawa da yafe wa juna a tsakanin mabiya addinai da ke yankin na Wukari, kuma ta haramta dukkan kungiyoyin mayakan sa-kai na kabilu tare da kwance musu damara da karbe dukkan makaman da ke hannunsu.
Kuma sun nemi a kafa wata rundunar sojoji da ’yan sandan kwantar da tarzoma a garin Wukari cikin gaggawa don magance masu son tayar da rikici a yankin. “Kuma a hana wadanda ke yin katsalanda ga ayyukan jami’an tsaro don ta haka ne kawai duk wanda aka samu da laifi za a iya hukunta shi komai matsayinsa,” inji sanarwar.
Musulmin sun ce ana hana ’ya’yansu shaidar takarda dan kasa tare da tauye musu duk damar da tsarin mulki ya ba su. Tare da kira ga gwamnatin jihar ta taimaka wajen sake tsugunar da al’ummar Musulmin Wukari da aka kone gidajensu.
Da yake tsokaci kan takardar koken ta Musulmi Mai bai wa Gwamna Darius Ishaku Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Silbanus Giwa ya ce Gwamnan ya dauki aniyyar ganin an maido da zaman lafiya a yankin Wukari. Mista Giwa ya nemi mazauna yankin su bai wa gwamnati goyon baya don cimma burinta na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a garin Wukari.