Musulmin Ghana sun yi tattakin neman a yi zabe lafiya
Musulmin Ghana sun yi tattakin neman a yi zaben kasar cikin zaman lafiya da adalci
Al’umar Musulmi a kasar Ghana sun yi tattaki dauke da kwalaye da aka rubuta kalaman zaman lafiya a jikinsu, da zummar ganin an yi zaben kasar cikin zaman lafiya da adalci.
Sarkin Zangon Mampong, birni na biyu a Jihar Ashanti na kasar, Alhaji Ahmad Usman ne ya jagoranci tattakin domin tunkarar zaben wanda za a yi a ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2020.
Muhammad Kamil Hashim wanda ya halarci tattakin ya shaida wa Aminiya cewa Musulmin sun yi tattakin ne a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba.
Ya ce za kuma a shirya taron kara wa juna sani a kan zaman lafiya a nan gaba kadan.
Ga kadan daga cikin hotunan yadda tattakin ya guda na.