Musulmin Laberiya sun koka kan tsarin addini

Wata sabuwar kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar Laberiya, ta bayar da shawarar cewa, gwamnatin kasar ta dauki addinin Kirista a matsayin addinin da al’ummar kasar ke bi.Wannan mataki bai yi wa al’ummar Musulmin kasar dadi ba, inda suka bukaci a sake shawara domin tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar kasar.A wani […]

Musulmin Laberiya sun koka kan tsarin addini
Musulmin Laberiya sun koka kan tsarin addini

Wata sabuwar kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar Laberiya, ta bayar da shawarar cewa, gwamnatin kasar ta dauki addinin Kirista a matsayin addinin da al’ummar kasar ke bi.
Wannan mataki bai yi wa al’ummar Musulmin kasar dadi ba, inda suka bukaci a sake shawara domin tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar kasar.
A wani mataki na nuna kin amincewa da wannan yunkuri, al’ummar Musulmin kasar Laberiya sun janye daga Majalisar Addinai ta kasar, majalisar da ke da karfin fada-a-ji ta fuskar samar da jituwa a tsakanin manyan addinan biyu.
A baya dai kasar Laberiya ta kasance a matsayin kasar da ba ruwanta da fifita wani addini, to amma daukar wannan mataki ya sa a yanzu tilas sai mutanen kasar sun yi muhawara don amincewa da sabon kudirin dokar kafin wannan kuduri ya zama doka.
Akasarin al’ummar Laberiya dai Kiristoci ne, sai dai akwai Musulmi da kididdiga ta nuna sun kai kashi 15 zuwa 20 cikin 100 na al’ummar kasar.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya