…Musulmin Najeriya sun koka kan taron kasa

Majalisar koli kan Al’amuran Addinin Musulunci a Najeriya ta gana da Shugaban kasa Dokta Godluck Jonathan inda ta koka masa game da fifikon da ta ce an ba mabiya addinin Kirista wajen zabar mahalarta babban taron kasa da ake yi.Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ne ya jagoranci shugabannin kungiyar zuwa Fadar Shugaban […]

…Musulmin Najeriya sun koka kan taron kasa
…Musulmin Najeriya sun koka kan taron kasa

Majalisar koli kan Al’amuran Addinin Musulunci a Najeriya ta gana da Shugaban kasa Dokta Godluck Jonathan inda ta koka masa game da fifikon da ta ce an ba mabiya addinin Kirista wajen zabar mahalarta babban taron kasa da ake yi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ne ya jagoranci shugabannin kungiyar zuwa Fadar Shugaban don gabatar da wannan koke a shekaranjiya Laraba.
Mabiya addinin Kirista 303 ke halartar taron, sabanin takwarorinsu Musulmi da aka ba su kujera 183.
Shugaba Jonathan ya tabbatar wa mambobin Majalisar koli ta Musuluncin cewa zai duba kukan nasu da idon basira, kuma zai kasance mai kamanta adalci a koyaushe.
A watannin baya, kungiyar Al’ummar Musulmin Kudu maso Yamma – MURIC ta yi korafin cewar babu Musulmi a cikin tawagar da za ta wakilci shiyyar.