Musulunci ba addinin zubar da jini ba ne!
Addinin Musulunci dai a lokacin da ya haramta kisan kai, ba wai yana haramta zubar da jinin muminai ba ne kadai! A’a yana kokarin kariya da tsare rayuwa da zubar da jinin dan Adam ne baki daya, Musulmi da kafiri. Saboda daga cikin kafiran su ma shari’ar Musulunci ta tabattar da kare musu jininsu da […]
Addinin Musulunci dai a lokacin da ya haramta kisan kai, ba wai yana haramta zubar da jinin muminai ba ne kadai! A’a yana kokarin kariya da tsare rayuwa da zubar da jinin dan Adam ne baki daya, Musulmi da kafiri. Saboda daga cikin kafiran su ma shari’ar Musulunci ta tabattar da kare musu jininsu da dukiyoyinsu a cikin dokokin Allah.
To, idan ya zamanto dokar da Allah Ya saukar ta haramta zubar da jinin wanda bai furta kalmar shahada ba, ta haramta zubar da jinin wanda ya ce Allah uku ne da kuma haramta zubar da jinin wanda ya ce Uzairu dan Allah ne, to, ke nan ta yaya kima da daraja da tsadar jinin wanda ya ce ya shaida babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Allah, kuma ya yarda Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne?
Hatta kafirai wadanda Musulmi suka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su ta tsawon wasu shekaru, a kan cewa ba za ku yaki juna ba a iya shekarun wannan yarjejeniya, to, haramun ne ga kowane Musulmi ya kashe daya daga cikinsu ko ya kwace dukiyar wani daga cikinsu, sai sun rushe wani sharadi daga cikin yarjejeniyar. Bayan haka kuma, ba za ku tallafa wa wasu ko wani a kan ya yake su ba. A’a irin wadannan dole ne ga Musulmi su tsare musu alkawarinsu na tsawon lokacin da suka yi alkawarin da su. Wanda kuwa ya kashe wani a lokacin wannan yarjejeniyar Manzon Allah (SAW), ya ce tsakaninsa da Aljanna tafiyar shekara dari biyar ne. Kuma wannan maganar ta bayyana a cikin Hadisi Sahihi.
To, idan fa aka duba a nan kafiri aka kashe ba Musulmi ba, to ina ga dan uwanka Musulmi! Wanda ka dauki bindiga da kowane irin dalili cikin dalilai ka raba shi da rayuwarsa, to kai kuma ka yi me a bayan kasa idan ka rayu din?
Kuma mu duba mu ga hatta wadanda kuke cikin yaki da kasarsu, an ce idan daya daga cikinsu ya nemi izinin zuwa kasarku, kuma kuka ba shi damar ya zo ya yi iya kwanakin da zai yi, to wajibi ne ku tsare masa jininsa da dukiyarsa har ya gama kwanakin da zai yi, kuma ku yi masa rakiya har zuwa inda zai ji ya amintu daga gare ku.
Wannan yana nuna kulawar shari’ar Musulunci da dokokin Allah dangane da tsadar rayuwar dan Adam.
Kuma ko yaki da aka shar’anta wa Musulmi, ba wai an hallata musu shi ne kawai don malalar da jinin kafirai ba, wannan ba ita ce manufar ba! Domin idan kafirai suka furta kalmar shahada bisa ga zabinsu, to, a nan dole sai a kyale musu jininsu, wannan ta sanya idan kafirai suka ki su furta kalmar shahada amma suka yarda da cewa za su shiga cikin “ammanarku” wato karkashin gwamnatinku, ku kuma ku kyale su a kan addininsu kuma kuka yarda da hakan. To, ba za ku kashe su ba. Ashe da manufar ita ce a yi kisa a zubar da jini, to, da idan aka fito yaki sai an kashe mutum koda ya yi kalmar shahada. Sai a ce ai an riga an fito a kan haka lokaci ya riga ya kure, me ya sanya bai Musulunta ba tun kafin a fito?
Haka kuma da manufar dai ita ce kisa da zubar da jinin dan Adam to, kuwa da babu yadda za a ce an samu kafiran amana wadanda za su zauna karkashin daular Musulunci, kuma a tsare musu jininsu da dukiyarsu ba tare da an ribace su ba.
Wannan ya nuna cewa addinin Musulunci addini ne da ke kare rayuwa, ba salwantar da rayuwa ba, duk wanda dokokin addini suka ce a salwantar da rayuwarsa, to idan ka duba za ka ga babu abin da ya fi dacewa sama da a salwantar da rayuwarsa din. Shi ya sa kafirai duk kafircinsu duk barnar da suka yi a bayan kasa, Allah Ya ce idan sun tuba suka tsayar da Sallah suka bayar da zakkah, to kada a kashe su kada a ribace su, to ina ga dan uwanka Musulmi wanda dama can shi Musulmi ne, yana Sallah, yana zakkah, yana karatun Alkur’ani da salati da istigfari gwargwadon iko, tare da haka ka ce za ka raba shi da rayuwarsa da wane dalili cikin dalilai?
Daga cikin masu kashe mutane akwai wadanda za su kashe mutum kawai domin su kwace dukiyarsa sawa’un a cikin gidansa ko a kan hanya lokacin da yake tafiya a kashe shi domin a kwaci dukiyarsa, to, wadannan Allah Ya fadi sakamakonsu a cikin Alkur’ani hukuncinsu shi ne a kashe su ko a tsire su ko a yanke musu kafar dama da hannun hagu ko kuma a kore su (a daure su) daga kasar Musulmi. Haka kuma, ’yan ta’adda wadanda su ba dukiyarka suke bukata ba, rayuwarka kawai suke son dauka, saboda kawai wata manufa ta duniya da suke fatar samu, sannan da tunanin watakila kana iya zamar musu barazana wajen samun abin da suke so.
Ka dai sani cewa, kowa dai ya kashe wani ko-ba-jima ko-ba-dade shi ma zai mutu.
Haka wani Balarabe mawaki yana fada a cikin wasu baitocinsa cewa:
“Da a ce ka rayu shekara dubu, kuma ka dada wasu shekara dubu biyu a kansu!
To, babu dai kokwanto a kan ranar nan wacce kai ma za ka tsinci kanka a kabari!”
Allah Ya shiryar da mu ga abin da yake So kuma Ya yarda shi, amin.
Muhammad Muhammad Abubakar (MMA) 08025866467