Musulunci da neman halal (1)
Fassarar Salihu Makera Gdodiya ta tabbata ga Allah, Muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba zuwa gare Shi. Muna rokonSa da’iman muna masu daga hannuwan kaskanci gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda kuma Y abatar ba […]
Fassarar Salihu Makera
Gdodiya ta tabbata ga Allah, Muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba zuwa gare Shi. Muna rokonSa da’iman muna masu daga hannuwan kaskanci gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda kuma Y abatar ba za ka sama masa maibinci mai shiryarwa ba.
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Shi ne Mamallaki kuma Gaskiya Mabayyani. Kuma na shaida lallai Shugabanmu Imaminmu Abin girmamawarmu, Macecinmu kuma Annabinmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa, mai gaskiyar alkawari amintacce. Ya Allah! Ka kara tsira da aminci da albarka a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa shugabanni masu kokari, zababbun na damansa, yarda Allah ta tabbata a gare su baki daya.
Bayan haka, yaku ’yan uwa muminai! Kamar yadda muka ce a Juma’ar da ta gabata – Allah Wanda albarka da daukaka suka tabbata a gare Shi – Ya yi umarni da neman halal da cin halal kuma Ya daure hakan da takawa. Kuma idan mumini ya jingina niyyarsa da himmarsa a jikin halal kuma ya a kan nemanta a wurin Allah, to lallai Allah Madaukaki Ya isar masa a kan haka, kuma zai azurta shit a inda ba ya zato. Sai Ya ce: “Wanda ya yi takawa ga Allah, Zai sanya masa mafita. Kuma Ya azurta shit a inda ba ya zato.” (Dalak: 2-3). kuma Ya ce: “Ku roke Shi daga fafalarSa.” (Ghafir:60). Kuma Ya ce: “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to lallai ne Ni ina kusa. Ina amsa kiran wanda ya yi kira. Don haka su amsa Min kuma su yi imani da Ni. La’alla za a shiryar da su.” (Bakara:186).
Manzonmu mai girma (Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi) kullum yana shriyar da mu zuwa ga abin da zai kusata mu da Allah da kuma Aljanna, kuma yana tsoratar da mu kana bin da zai nesanta mu da Allah. Babu wani abu da zai kusanta mu da Allah da kuma Aljanna face ya umarce mu da shi (Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi). Kuma babu abin da zai nesanta mu da Allah ya nesanta mu da Aljanna face ya gargade mu a kansa. Shi Manzon rahama ne, Allah Madaukaki Yana cewa wajen siffanta shi. “Ba Mu aike ka face rahama ga halittu.” (Anbiya: 107). Kuma (SAW) ya kasance yana cewa: “Bawa bai ci wani abinci ba mai alheri irin abin da ya yi aiki da hannunsa. Kuma lallai Annabin Allah Dawud (AS) ya kasance yana ci daga aiki hannunsa.”
Don haka muka ce: “Lallai neman halal farilla ne a bayan farilla, kuma muka ce shi wajibi ne a kan kowane Musulmi, bisa hukuncin Manzon Allah (SAW). Don haka ne sahabbai lokacin da suka isa Madina suka kasance sun hijira sun bar dukiyoyinsu a Makka, wadansu sun baro bisa radin kansu wadansu bisa tilas kamar Suhaibu (RA) wanda aka ba shi zabi kan ya yi hijira ya bar dukiyarsa ko ya rike dukiyarsa ya zauna a Makka ba tare da ya yi hijira ba, sai ya zabi ya yi hijira ya bar dukiyar a bayan bayansa.
To lokacin da sahabban suka isa Madina a halin da muka ambata, al’amarinsu ya daidaita a Madinatul Munawwara, kowannensu sai ya shagaltu da abin da zai iya yi. Daga cikinsu akwai wanda ya kama aikin gona, daga cikinsu akwai wanda ya kama kasuwanci da kuma wadanda suka kama wasu ayyuka na daban da suka shafi harkokin tafiyar da al’umma kamar tara Zakka da aiki a kanta da jihadi al’amarin da ya shafe su gaba daya, wanda shi ma daya ne daga cikin hanyoyin neman halal.
A lokacin da ka shagala da sabubba ka yi riko da su, Musulunci- yana umarni da yin nasiha a cikinsu,yana umartarmu mu kasance masu gaskiya a cikin komai, a cikin saye da sayarwa a cikin noma da a cikin sana’a. Domin lallai shi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi mana algushu ba ya daga cikinmu.”
Don haka ya wajaba a kan Musulmi ya kasance mai nasiha, idan kai ma’aikaci ne da kake noma a gonar mutum ka yi nasiha ka yi gaskiya, in kai dan kasuwa ne ka yi gaskiya kai kowane aiki kake yi da kake samun amfani ka yi gaskiya a cikinsa ka yi nasiha domin Allah.
Ka sani lallai kai kana cikin ibada ce, domin Manzon Allah (SAW) ya tabbatar ga wanda yake kasuwanci ko yake aiki yake neman halal cewa lallai wannan aiki nasa nau’i ne na ibada. Idan ya kasance mutum ya shiga kasuwa don neman na kansa ibada ce, haka don ya wadatar da iyalinsa ibada ce, ko ya kare dansa kai hatta ya wadatar da masu yi masa hidima hakan ibada ce. Don wanda ya yi aiki don wadatar da kansa daga mutane ko iyalinsa ko dansa ko mai yi masa hidima ko abokinsa sadaka ce. Duk abin da ka ci ko ka ciyar da iyalanka ko ka ciyar da ’ya’yanka kon ka ciyar da masu yi maka hidima du kana ana rubuta maka sadaka a kai, alhali ka amfana da shi. Me ya kai girman ni’imar Allah Madaukaki a kan bayinSa! Shi ne Wanda Yake bayar da ni’ima kuma Yake sanya albarka a cikinta, mu kuma muna amfana da ita amma ana ba mu lada a kanta. Me ya kai girman wannan ni’ima! Kuma duk lokacin da muka yi godiya a kara mana.
Sayyidina Sa’ad bn Abu Wakkas (RA) ya ce: “Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Ka yi min wasiyya ya nanata.” Sai (SAW) ya ce: “Ka guji abin hannun mutane, kuma ka guji kwadayi. Domin shi talauci ne mai halartowa. Kuma ka guji abin da za a ta’azzara daga gare shi.”
Abubuwa uku, na farko: Kada ka yi kwadayi har abada a cikin abin hannun mutane, domin kwadayin abin hannu mutane zai cika zuciyarka da bakin ciki, ya sanya ka a cikin mutanen da ba su da kima, babu wanda zai girmama ka. Hatta zuhudu ba zai tabbata ba, sai da barin abin da ke hannun mutane. Manzon Allah (SAW) yana fadi kan wannan babi. “Ka guji duniya, Allah Ya so ka, kuma ka guji abin hannun mutane, sai mutane su so ka.”
Don haka ba makawa mu yi aiki da wasiyyar Manzon Allah (SAW), ta wajen barin ta’allaka da abin hannun mutane. Sai dai kuma muna bukatar ci da sha, don haka abin da ya wajaba a kanmu shi ne mu yi aiki a kowane bangare na rayuwa. Allah Madaukaki Ya sanya wa kowane abu sababi (hanya), ya sanya maka kai dan Adam hanyar isa ga komai. Ga hanyoyi nan da dama, sai dai ka yi tattali tare da lura da hanyar halal. Ka nemi duk abin da za ka nema, kuma ka guji kwadayi, ka guji ta’allaka da abin hannun mutane, ka guji duk wani abu da za ka wahala a kai. Ka aikata shi sannan ka dawo wurin mutane kana cewa: “Wallahi na yi nadama. Da na sani da ban fadi haka ba, ko da na sani da ban aikata haka ba.” Domin Allah Ya azurta ka da hankali don ka rika auna maganar da za ka furta, kuma Ya ba ka fahimta domin ka rika bambance aikin da za ka yi. Don wata magana ko wani aiki da za ka aikata ya jawo maka nadama har ka rika neman uzuri ga mutane, to Manzon Allah (SAW) ya umarce ka da kada ka aikata shi to farko, don haka ka guje shi.
Idan mutum ya wadatu da abin da Allah Ya ba shi, sai ya samu wadatar zuci a Hadisin Jabir (RA) SAW ya ce:”Wadatar Zuci taska ce daba ta karewa.” Ma’ana wadatuwa da abin da Allah Ya azurta ka task ace marar iyaka, amma sai ka rika wahalar da kanka cikin abin da ke hannun mutane. Ka wahalar da kanka idan ka rika kwadayin abin da ba za ka samu ba, ko ba za ka isa gare shi ba ta hanyar ajali ko dukiya.
Don haka ne a wani Hadisin Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Ka yarda da rabon da Allah Ya ba ka, sai ka zamo mafi wadatar mutane.” Kuma a cikin wani Hadisin Manzonmu Mai girma (SAW) ya ce: “Wanda ya wayi gari cikin aminci kuma mai lafiya a jikinsa yana da abincin wannan wuni, to kamar duniya da kayan alatunta ta tattaru masa ne!”
Don haka wanda ya wayi gari cikin aminci da zaman lafiya lafiyayye a jikinsa da zuciyarsa, ya wayi gari lafiyayye daga dukkan cututtuka ko raunuka a jikinsa, kuma yana da abincin wannan wuni abincin safe da na rana da na dare, idan yana da wannan to ya yi imani kuma ya gode wa Allah. Domin matsayinsa kamar matsayin wanda aka tattaro masa duniya daga kowane sashi da kayan cikinta da daukakarta. Kamar dai ka samu komai daga sassan duniya, kamar ka samu komai mai daukakar daraja a wurin mutanen da suke cikin duniya. Haka Manzo Mai girma (SAW) yake yi mana nasiha yana ji mana tsoro daga makalewa a bayan Shaidan.
Kuma lallai komai shagulguka ka tabbatar ka shagaltu da yi wa Allah aiki. Duk yadda shagaltuwa ta kai kada ta raba ka da zikiri da ambaton Allah da yin tasbihi ga Allah. Manzon Allah (SAW) yana cewa- ga wanda yake aiki a kasuwa – “Idan dayanku ya shiga kasuwa kuma ya ce: “La’ilaha illallahu wa hadahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, yuhyi wa yumitu wa huwa hayyun la ya mutu, biyadihil khaira, wa huwa ala kulli shai’in kadir.” Allah Ya rubuta masa kyakkyawan aiki dubu dubu, kuma Ya shafe mummunan aiki dubu dubu, kuma Ya daukaka darajarsa da shi dubu dubu, kuma Ya gina masa gida saboda hakan a cikin Aljanna.” Tirmizi ya ruwaito, sai dai ya ce Hadisin garibi ne, amma Hafiz Ibn Munzir ya ce: “Isnadinsa bai yanke ba kuma mazajensa masu amana ne.” Don haka Hadisin ingantacce ne.
Ka duba kana tafiya kasuwa idan ka samu riba da ciniki falillahil hamdu, sai ka gode maSa Ya kara maka. Idan ba ka samu komai a kasuwar ba, ka fadi wadannan kalmomi ka samu wadannan kyawawan ayyuka shin ba ka ci riba ba?