Musuluntar da ’yan matan Chibok: Ba Musulunci ba ne –kungiyoyin Musulunci da siyasa

kungiyoyin Musulunci sun soki yadda kungiyar Boko Haram ta musuluntar da ’yan matan Chibok da ta sace daga makaranta fiye da wata daya ya ta gabata, inda suka ce hakan ya saba wa koyarwar Musulunci, wadda ta hana tilasta wa wani shiga addinin.kungiyoyin da suka soki wannan lamari sun hada da kungiyar Kare Hakkin Musulmi […]

Musuluntar da ’yan matan Chibok: Ba Musulunci ba ne –kungiyoyin Musulunci da siyasa
Musuluntar da ’yan matan Chibok: Ba Musulunci ba ne –kungiyoyin Musulunci da siyasa

 ’Yan matan Chibok da Boko Haram suka sace wata daya daga ya gabata.kungiyoyin Musulunci sun soki yadda kungiyar Boko Haram ta musuluntar da ’yan matan Chibok da ta sace daga makaranta fiye da wata daya ya ta gabata, inda suka ce hakan ya saba wa koyarwar Musulunci, wadda ta hana tilasta wa wani shiga addinin.
kungiyoyin da suka soki wannan lamari sun hada da kungiyar Kare Hakkin Musulmi (Muslim Right Concern -MURIC) da kuma kungiyar dalibai Musulmi ta Najeriya (MSS), yayin da Jam’iyyar APC ta nuna rashin amincewarta da hanyar da ’yan Boko Haram din suka bi wajen musuluntar da ’yan matan.
A ranar Litinin ne, Shugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnati Lid Da’awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ya fitar da wani faifain bidiyo inda a ciki aka nuna ’yan mata 130 sanye da hijabi suna karanta wasu ayoyi daga Alkur’ani Mai girma a wani wuri da ba a bayyana ba, kuma ya bayyana cewa da dama daga cikinsu sun musulunta.
Abubakar Shekau, wanda ya bayyana cikin kayan soja, bai fadi yawan daliban ba, sai dai ya ce da yawa daga cikinsu sun musulunta, yayin da kalilan suka ki.
Faifan bidiyon mai tsawon kusan minti 30, inda ya dauki lokaci mai tsawo yana jawabi cikin harshen Larabci kafin ya karashe da Hausa, ya ce cikin Larabci “Wadannan ’yan mata da muka kama daga makarantar boko, kuma (Shugaba) Obama (na Amurka) da Holande na Faransa da Jonathan (na Najeriya) suke hana idonsu barci a kansu, sun riga sun musulunta. Hakika sun riga sun shiga addinin Musulunci, sun bar addinin Kirista. Wallahi, sun shiga Musulunci da kansu, sun yarda babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma sun yarda Annabi Muhammad Manzon Allah ne, kuma lallai Isa Manzon Allah ne kuma Kalmar Allah ne…”
Shekau ya kuma ce baya ga wadannan ’yan mata akwai wasu da suka kama, kuma ba za su sako ’yan matan ba, sai idan Gwamnatin Tarayya ta sako ’ya’yan kungiyarsu da ke tsare a sassan kasar nan, kuma ya ce zai iyar da barazanarsa ta sayar da ’yan matan da ba su musulunta ba.
A cikin faifan bidiyon an nuno ’yan matan suna karanta kalmar shahada da surar Fatiha, sannan aka sanya uku daga cikinsu, wadanda biyu suka musulunta, suka bayyana dalilin musuluntarsu, yayin da dayar, wadda da ma Musulma ce, ta bayyana ganewarta da illar karatun boko.
’Yan matan biyu, wato Hauwa Abdu, wadda sunanta na yare shi ne Kwantai kuma yanzu ake kiranta Halima da Saratu Sonji, wadda ake kiranta Sa’adatu yanzu ,wadda ta ce ta fito ne daga unguwar Bakin Kasuwa sun bayyana cewa, sun musulunta ne a kashin kansu ba tare da an tilasta su ba, inda suka nemi iyayensu su rungumi Musulunci su bar addinin Kirista domin tsira gobe kiyama. Ita kuwa Hajara Isa, wadda Musulma ce, ta ce a yanzu ta gane ilimin boko haram ne, kuma za ta shaida wa iyayenta cewa hanyar da suke bi ba ta da kyau. Kuma ta yi addu’ar Allah Ya shiryar da su.
Sai dai a martaninta, kungiyar MURIC ta ce tubar da ’yan matan ya saba wa Musulunci.  “Mun yi tir da da’awar an musuluntar da ’yan matan da aka sace, wanda yin haka raganci ne, abin kunya ne, tabargaza ce, rashin hankali ne kuma haramtacce ne.”
kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa dauke da sanya hannu Babban Daraktanta, Farfesa Is’hak Akintola. Ta kara da cewa: “Muna tabbatarwa cewa irin wannan musuluntarwa ba ta da madogara a karkashin Musulunci, saboda wanda ba Musulmi ba, yana musulunta ne bisa radin kansa ko kanta. Kuma ba mu da wata shakka cewa wadannan ’yan mata an musuluntar da su ne bisa tilastawa, don haka wannan ‘musuluntarwa’ haramtacciya ce a karkashin shari’a domin Allah Madaukaki Ya ce a cikin Alkur’ani Mai girma: “Babu tilastawa a cikin addini.”  (k:2:256).
Haka nan kungiyar ta MURIC ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da tayin Shekau na musayar ’yan Boko Haram din da ake tsare da su da ’yan matan da suka sace, inda ta ce zai yi wahala ya cika wannan alkawari.
MURIC ta zargi Boko Haram da kokarin jirkitawa da bata kyakkyawar koyarwar Musulunci, inda ta bayyana ’yan Boko Haram da ’yan tawaye kuma makiya zaman lafiya.
Ta bukaci a gudanar da addu’o’i a coci-coci da masallatai don ganin bayan kungiyar, inda ta bukaci sojojin Najeriya su koma su sake dabarun yadda za su murkushe kungiyar.
A nasa bangare, Shugaban kungiyar dalibai Musulmi ta kasa (MSSN), Kaamil Kalejaiye ya ce kungiyar ta kasa gane manufar kashe mutane barkatai da ke gudana a kasar nan da sunan addini. “Kashe mutane haka siddan a kasarmu ya wuce iyaka, kuma Musulunci ne ke asara a karshe. Mun la’anci wadannan kashe-kashe da sace mutane da duk wani nau’in hari kan jama’a. Kuma muna la’antar masu shirya hakan da babbar murya,” inji shi.
Ya ce: “Musulunci addini ne na zaman lafiya kuma ta kowace hanya bai amince a kashe ko a sanya bam ko a sace mutane tare da tilasta su shiga cikin addinin ba.”
Ita ma Jam’iyyar APC ta yi Allah wadai da musuluntar da wasu daga cikin ’yan matan Kiristoci da Boko Haram suka sace wata guda da ya gabata.
ShekauWata sanarwa da ta fitar a Abuja a ranar Talata bayan taron gaggawa kan batun Boko Haram, jam’iyyar ta ce hakan ba abin lamunta ba ne, kuma ya saba wa tsarin mulki, kuma tilasta wani ya karbi wani addini abu ne da ya zama wani dabbanci.
“Wannan dambarwa ta sace ’yan matan ta doki zuciyar kasarmu. Kuma a yayin da muke ci gaba da ganin miyagun ayyukan Boko Haram, sai ga shi mun wayi gari da wani sabon abin baki ciki game da kananan ’yan matan, wadanda a kaikaice aka tsaya kansu da bindigogi aka tilasta musu karbar addinin Musulunci,” inji jam’iyyar.
Ta kara da cewa: “Wannan abu ne mai daga hankali, abin bakin ciki ne, ba za a lamunce shi ba ta kowace fuska, kuma muna Allah wadai da hakan da dukkan karfinmu,” inji APC.
Jam’iyyar ta bukaci gwamnati ta tsaya a natse ta nazarci faifan bidiyon na baya-bayan nan da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya saki, domin ganin wane mataki za ta kara dauka kan kokarin da kasashen duniya ke yin a ganowa da kubutar da ’yan matan.
“Mun sha fadi cewa ba za a kauce wa wasu hanyoyi na tattaunawa da sulhuntawa ba domin kubutar da kasarmu daga hannun wadannan ’yan ta’adda tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayukan jama’ar kasarmu.  Don haka muna shawarta gwamnati ta bi duk hanyar da ta dace domin ganin an kubutar da wadannan ’yan mata su koma ga iyayensu lafiya,” inji APC.
’Yan mata da akasarinsu Kiristoci ne an sace su ne daga Sakandaren Gwamnati ta Chibok da ke Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilun da ya shige.
 Kuma Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya ce iyayen ’yan matan da aka sacen, sun tabbatar da 54 daga cikin wadanda Boko Haram ta nuna a faifan bidiyo na baya-bayan nan, ’ya’yansu ne.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin taron manema labarai da kungiyar fafutikar a sako ’yan matan mai taken “Bring Back Our Girls” da suka yi takakkiya zuwa masaukin baki na gwamnatin Jihar Borno da ke Abuja.
Gwamna Shettima ya ce ’yan mata 54 da ke cikin bidiyon iyayensu sun gano su ta fadin sunayensu ta hanyar wani nunin bidiyon da aka yi, wanda ya hada da wasu iyaye da daliban da suka tsira daga kamun tun farko.
Ya ce, wasu malamai da jami’an tsaro da jami’an gwamnatin Borno, a karkashin jagoranci Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Abubakar Kyari ne suka gudanar da aikin tantancewar, bayan da gwamnati ta gayyaci iyayen da daliban zuwa gidan gwamnatin don tantance su daga cikin bidiyon da aka nuna.
Kuma ya ce adadin wadanda ake ganowar yana karuwa yayin da tantancewar ke ci gaba da gudana.
Daga cikin wadanda aka gano a cikin faifan bidiyon kamar yadda Kakakin Gwamnan Isa Umar Gusau ya saki sun hada da:
Agnes Gafane da Saraya Stober da Hauwa Bitrus da Hajara Isa da Na’omi Philimun da Hauwa Abdu (wadda ta fara magana a bidiyon) da Magret Yama da Shitta Abdu da Jummai Muta.
Sauran su ne Ladi Paul da Roda Peter da Filo Dauda da  Godiya Bitrus da  Saratu Tauji (ta biyu da ta yi magana a bidiyon) da Ross Daniel da Hauwa Ali da  Hajara Isa (ta uku da ta yi magana a bidiyon) da Luba Afga da Na’omi Luka da  Saraya Emos Ali da Bilkisu Abdullahi da kuma Mairama Ali.
Akwai kuma Maryam Ali Maiyanga da Dabora Abbas da Kabu Mala da Halima Ali da Yana Bukar da Solomi Pugu da  Lydia Emmar da Luba Sanda da Saraya Samuel da Comfort Habila da Rejoice Shanki da Gloria Yaga da Mary Nkeki da Moda Baba da kuma Hauwa Isuwa.
Sauran sun hada da Patient Jacob da Ladi Jajel da Abigel Bukar da Fanta Lawan da Zainabu Yaga da A’isha Lawan Zanna da Dokas Yakubu da Kabu Mala da  Maryama Bashir da Hauwa M. Maina da Mary  G. Dauda da  Susana Yakubu da  Maryam Abbas da Laraba John da  Hanatu Nuhu da Na’omi Bukar da kuma Rifkatu Galang.
Kakakin Gwamnan ya ce ana tantance sunayen ta duba su da wadanda ke makarantar da kuma wadanda aka bayyana a kwanakin baya don tabbatar da gaskiyarsu.