Mutane 11 sun makale a gini hawa uku da ya rushe a Anambra
Kimanin mutane 11 ne suka makale a wani ginin hawa uku da ya rushe a garin Nnewi jihar Anambra a safiyar yau Alhamis. Ginin dai yana yankin Okpuno unguwar Otolo, dake karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Haruna, ya tabbatar da […]
Rushewar wani gini
Kimanin mutane 11 ne suka makale a wani ginin hawa uku da ya rushe a garin Nnewi jihar Anambra a safiyar yau Alhamis.
Ginin dai yana yankin Okpuno unguwar Otolo, dake karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Haruna, ya tabbatar da aukuwar rushewar ginin wanda mallakin Collins Avoyi ne.
Haruna ya kara da cewa, a yanzu haka an ceto 9 daga cikin 11 yayin da ake kokarin ceto sauran. Wadanda aka ceto an kaisu asibiti.