Mutane 12 daga cikin 416 da Boko Haram ta sace sun tsere — BOSYA
A kwanakin baya ne aka ruwaito cewa ƙungiyar Boko Haram ta kai hari kan sansanin sojoji a Ngoshe, inda ta ƙona motocin aikin jami’an tsaro, ta kashe mutane da ba a tantance adadinsu ba, sannan ta sace mazauna garin 416.
Kungiyar matasan Kudancin Borno (BOSYA) ta tabbatar da cewa, kimanin mutane 12 daga cikin mutane 416 da Boko Haram ta sace a Ngoshe, wani gari a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno sun tsere daga hannunsu.
A dai ranar 4 ga Maris, 2026 an ruwaito cewa ƙungiyar Boko Haram ta kai hari kan sansanin sojoji a Ngoshe, inda ta ƙona motocin aikin jami’an tsaro, ta kashe mutane da ba a tantance adadinsu ba, sannan ta sace mazauna garin 416.
- Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika
- Tsananin zafi ya sa iyalai kwana a waje, sana’o’i na rushewa a Kano
Rahotanni da suka gabata a ranar 10 ga Afrilu sun nuna cewa ƙungiyar matasan Borno ta Kudu ta yi magana da manema labarai kuma ta yi aiki a matsayin mai shiga tsakani tsakanin ƙungiyar ‘yan ta’addan da waɗanda abin ya shafa, inda Boko Haram ta nuna mutanen da aka sace.
Shugaban ƙungiyar matasan Borno ta Kudu, Samaila Kaigama, ya raba bidiyon waɗanda aka kama da suka tsere da kuma wata sanarwa da wata jaridar da ba Aminiya ba ta wallafa ta WhatsApp a ranar Laraba.
A cikin sanarwar, Kaigama ya ce: “ƙungiyar matasan Kudancin Borno (BOSYA) tana farin cikin sanar da cewa waɗannan mata da yara waɗanda aka keɓe a Ngoshe sun tsere kuma yanzu haka suna cikin aminci a wani gari da ke kusa.”
Ya ce waɗanda suka tsere sun ƙunshi mata 11 da namiji guda.
“Duk da cewa muna godiya da wannan ci gaban, dole ne mu bayyana a sarari cewa ana kyautata zaton cewa akwai adadi mai yawa na waɗanda abin ya shafa a hannunsu.”
ƙungiyar ta bayyana cewa an ɓoye ainihin wurin da waɗanda suka tsere suka isa saboda dalilan tsaro.