Mutane 14 Jihar Adamawa ta rasa a Hajjin bana

Akalla mutane 14 ne daga cikin mahajjatan bana daga Jihar Adamawa suka rasa rayukansu a yayin aikin Hajjin da ya gabata. Injiniya Umar Bobboi, Sakataren Hukumar Alhazai na jihar ne ya bayyana haka, a lokacin da yake gabatar da ruhotanni game da ababen da suka afku a hajjin bana da ya gabata. Ya kara da […]

Mutane 14 Jihar Adamawa ta rasa a Hajjin bana
Mutane 14 Jihar Adamawa ta rasa a Hajjin bana

Akalla mutane 14 ne daga cikin mahajjatan bana daga Jihar Adamawa suka rasa rayukansu a yayin aikin Hajjin da ya gabata.

Injiniya Umar Bobboi, Sakataren Hukumar Alhazai na jihar ne ya bayyana haka, a lokacin da yake gabatar da ruhotanni game da ababen da suka afku a hajjin bana da ya gabata. Ya kara da cewa akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu a turmutsin da aka yi wajen jifar shedan kuma mutane uku a wurare daban-daban, sannan kuma mutane biyu suka bata.
Ya ce a cikin mutane 14 nan da suka rasa rayukansu, mace daya ce kawai a cikinsu, sauran kuma maza ne.
Jihar Adamawa ta nada wata kungiya wadda za ta kai ziyarar ta’aziya a gidagen wadanda suka rasa rayukansu. Kuma kungiyar za ta ba da katin shedar mutuwar kowane marigayi ga iyalinsa, kamar yadda hukumar Saudiyya ta bayyana. Haka kuma, hukumar ta yi addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu a bam din da ya tashi a masallacin Jambutu.
Bayan an gama taron ne Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Adamawa, Ahmad Sajoh ya bayyana wa manema labarai cewa jihar ta yi na’am da sanya hasken wutar lantarki a bakin titunan jihar.
Ya kara da cewa za a daura wadannan fitilu ne a hanyoyin masallatai da kasuwa da kuma inda mutane suka fi taruwa, domin su hango ’yan Boko Haram a duk lokacin da suka yi kokarin kai musu hari.