Mutane 16 sun kone kurmus a hatsarin mota a Ondo —FRSC

Ana kyautata zaton daya daga cikin motocin tana dauke da man fetur a lokacin da hatsarin ya auku

Mutane 16 sun kone kurmus a hatsarin mota a Ondo —FRSC

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane 16 da suka kone kurmus a wani hatsarin mota da ya auku a ranar Talata a Jihar Ondo.

Kwamandan hukumar a jihar, Mista Samuel Ibitoye, ya ce yanzu haka mutane biyar da suka samu munanan raunuka a hatsarin suna kwance asibiti likitoci na kokarin ceton rayukansu.

Ya ce hatsarin ya auku ne a kauyen Ajue da ke kan hanyar Ondo zuwa Ore cikin Karamar Hukumar Odigbo a tsakanin wata bas kirar Toyota Hiece da tirela kirar Man Diesel.

Kwamanda Ibitoye ya ce ana kyautata zaton daya daga cikin motocin tana dauke da man fetur a lokacin da hatsarin ya auku, wanda hakan  ya haifar da tashin gobara a nan take da kuma konewar mutane 16 kurmus.

Ya ce jami’ansa sun shafe kimanin awa 4 suna gudanar da aikin ceton rayuka da kawar da burbushin tokar kayan da suka kone da bude hanyar ga masu zirga-zirgar abubuwan hawa.

Ibitoye ya ce har zuwa ranar Laraba ba su iya gano ainihin dalilin da ya haifar da wannan hatsari ba, amma a cewarsa, suna kyautata zaton gudun wuce kima da kokarin yin Overtaking shi ne musabbabi.

Ya yi kira ga masu tuki da su kauce daga yin gudun wuce kima kuma su girmama dokokin hanya domin tsira da rayukan bil’adama.

Tags