Mutane 20 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Kogin Binuwai

Ana fargabar mutane akalla 20 sun rasu a wani hatsarin kwalekwale a Kogin Binuwai a ranar Asabar.

Mutane 20 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Kogin Binuwai

Yadda masu kwalekwale ke tsallakar da fasinjoji

Ana fargabar mutane aƙalla 20 sun rasu a wani hatsarin kwalekwale a Kogin Binuwai a ranar Asabar.

Mata da ƙananan yara ne akasarin fasinjojin kwalekwalen da ya kife ya yi ajalinsu a kusa da yankin Ocholonya da ke Ƙaramar Hukumar Agatu da ke jihar.

Aminiya ta gano cewa matafiyan sun gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta komawa gidajensu a yankin Doma na Jihar Nasarawa bayan sun gama cin kasuwa a yankin Ocholonya.

Wani mazaunin yankin ya shaida mana cewa “babu wanda ya tsira daga cikin mutanen da kwalekwalen ya kife da su a hanyar komawa yankin Odenyi da ke Jihar Nasarawa.”

A ranar Lahadi Shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu, Melvin James, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa yawancin fasinjojin ’yan kasuwa ne daga yankunan Apochi da kuma Odenyi na Ƙaramar Hukumar Doma ta Jihar Nasarawa.

“Na samu labarin yiwuwar mutane 20 ne suka mutu. Masunta sun gano gawarwakin, amma ina dai jiran tabbataccen bayani a hukumance game da yawan mamatan,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ana ƙoƙarin ganin Rundunar Sojin Ruwa ta shiga aikin ceto a yayin da ake kokarin haɗa kai da hukumomin jihar Nasarawa domin jajanta wa iyalan mamatan.

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899