Mutane 2,000 sun mutu a girgizar kasa a Afghanistan
Ana fargabar girgizar kasar ta shafe wasu kauyuka 12, kuma adadin mamatan zai karu, bayan dubban da suka ji rauni
Girgiziar kasa da ta auku a ranar Asabar ta yi ajalin mutane akalla dubu biyu a Lardin Herat, a cewar hukumomin kasar.
Wani babban jami’in gwamnatin Taliban ta kasar ya ce ana fargabar adadin mutanen zai karu, a girgizar kasar wadda ita ce mafi muni a shekaru 20 da suka wuce.
- Takardun Tinubu: Babu ruwan Kwankwaso da karar da Atiku ya shigar —NNPP
- Ya datse hannuwan mahaifiyarsa da adda saboda rashin jituwa
Akalla kauyuka 12 ne girgizar kasar mai karfin maki 9.3 ta rushe su a kusa da Lardin Herat a yayin da dubban mutane suka samu raunuka.
Kakakin gwamnatin Taliban da ke kasar Qatar, Suhail Shaheen, ya shaida wa Al Jazeera ya ce mutane da dama sun bace a yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan girgizar kasar.
Ya kara da cewa ana bukatar tantuna da kayan abinci da magunguna cikin gaggawa, inda ya yi kira ga kamfanonin cikin kasar da kungiyoyin kasa da kasa su taimaka wa jama’a.