Mutane 25,490 Isra’ila ta kashe a Gaza —Ma’aikatar Lafiya

Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 25,490 wasu 63,354 suka samu raunuka a Gaza

Mutane 25,490 Isra’ila ta kashe a Gaza —Ma’aikatar Lafiya

Ma’aikatar Lafiya a Gaza ta ce Falasdinawa akalla 25,490 aka kashe wasu 63,354 suka samu raunuka, tun bayan barkewar yaki a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce adadin na baya-bayan nan ya hada da mutuwar mutane 195 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a yankin Falasdinawa a yakin Isra’ila da kungiyar Hamas.

A kimanin kwanani 107 ken nan yakin Isra’ila a Gaza ya yi ajalin Falasdinawan, wadanda kawo yanzu sama da miliyan 1.7 daga cikinsu sun rasa muhallansu.

Hukumomin lafiya na duniya sun bayyana cewa halin da al’ummar Gaza  suke ciki ya kai inna-naha, kuma suna matukar bukatar a kawo musu dauki.

Aminiya ta ruwaito cewa a Rundunar Sojin Isra’ila ta koka da cewa a ranar Litinin mayakan Hamas sun kashe adadi mafi yawa na sojojinta a Gaza.

A ranar Talata Rundunar ta sanar cewa ba a taba yi wa sojojinta masu yawa haka kisa a rana guda ba, tun da suka fara kai samame a Gaza a watan Oktoban 2023.

Wannan ragargazar da sojojin na Isra’ila suka sha na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin ganin an samu maslaha a rikicin kuma a daidai lokacin da wani babban jami’in gwamnatin Amurka za je yankin, domin sanya baki a sako karin mutane da aka yi garkuwa da su.

Ofishin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya sanar cewa musayar wuta ta tsananta a Gaza, sakamon samamen Isra’ila a yankin Khan Yunis.OCHA ya ce sojojin Isra’ila sun kai hari da makaman atilare da jirage marasa matuka kan babban ofishinsaa da ke Khan Yunis inda suka jikkata mutanen da suka samu mafaka a harabar ofisihin.