Mutane 30 sun bace sakamakon kifewar kwalekwale a Anambra
Akalla mutane 30 ne ake fargabar sun bace bayan wani jirgin ruwan fasinja ya kife a garin Umunnankwo da ke Karamar Hukumar Ogbaru ta Jihar Anambra.
Akalla mutane 30 ne ake fargabar sun bace bayan wani kwalekwalen fasinja ya kife a garin Umunnankwo da ke Karamar Hukumar Ogbaru ta Jihar Anambra.
Wani ganau, jirgin ruwan da ke fama da matsa, yana dauke da mutane kusan 85 a lokacin da ya kife a Juma’a, 7 ga Oktoba, 2022.
- Zulum ya bai wa asibiti tallafin N100m da gidaje 24
- Uba ya ba ’yar cikinsa kwaya, ya yi mata fyade a Ogun
Ya ce kwalekwalen ya yi hastarin ne bayan ya tashi ne daga Gadar Onukwu zuwa kasuwar Nkwo, Ogbakuba duka a Ogbaru.
Ya ce, kawo yanzu, rahotannin da ba na hukuma ba sun nuna cewa tsakanin mutane 20 zuwa 30 har yanzu ba a gan su ba bayan aukuwar hatsarin.
Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na Karamar Hukumar Ogbaru, Honorabul Pascal Aniegbuna, ya ce an ceto wasu daga cikin fasinjojin yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu.
A cewarsa, lamarin babban abin takaici ne.
A halin yanzu, tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Ogbaru, Honorabul Victor Afam Ogene ya bayyana matukar damuwa bisa abin da ya faru.