Mutane 30 sun mutu a harin ’yan ta’addan Katsina
Akalla mutane 30 aka kashe wasu da dama na asibiti sakamakon hare-haren ’yan bindiga a kauyukan Dutsinma da Safana a Jihar Katsina
Akalla mutane 30 aka kashe wasu da dama na karbar magani a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, sakamakon harin ’yan bindiga a kauyukan Dutsinma da Safana.
Wasu ’yan bindiga a kan babura ne suka kai wa kauyukan farmaki a ranar Talata, kamar yadda kafar yada labarai ta Katsina Times ta bayyana.
’Yan fashin sun kai harin ne a kauyuka Tashar Kawai Mai Zurfi, Sabon Gari Unguwar Banza, Dogon Ruwa, Sanawar Kurecen Dutsi, Unguwar Bera, Kuricin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru da kuma Ashata.
Sauran al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Unguwar Ido, Kanbiri, Kunamawar Mai Awaki, da Kunamawar ’Yargandu da ke Karamar Hukumar Safana.
- Yadda Sallar Layya za ta kasance a Najeriya da Saudiyya
- NAJERIYA A YAU: Me Manoma Suka Shirya Wa Daminar Bana?
Har ila yau, a daren Laraba da safiyar Alhamis, maharan sun sake kai wa garuruwan Dogon Ruwa, ‘Yar Kuka, Rimi, Lezumawa, da sauran kauyukan da ke kusa da Safana da ke kan iyaka da Dutsinma.
Mazauna kauyuka sama da 15 ne suka tsere daga gidajensu, inda suke neman mafaka a garin Dutsinma da kauyen Turare sakakamkon harin barazanar ’yan.
Hare-haren ‘yan bindiga na kara kamari a wasu sassan jihar Katsina, inda a baya-bayan nan aka samu rahoton faruwar lamarin a yankunan Batsari, Kankara, Malumfashi da Faskari.
Kokarinmu na samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya faskara, domin har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoton, ba a samu lambar wayarsa ba, kuma bai masa rubutaccen sakon da aka aika masa ba.