An kashe mai juna biyu a turereniyar sayen shinkafar kwastam
An kashe mace mai juna biyu da wasu mutane shida, wasu da dama sun jikkata a wurin sayen shinkafar da hukumar Kwastam ta yi wa jama’a gwanjon ta
Mutane bakwai, ciki har da mace mai juna biyu sun rasu a yayin turereniyar sayen shinkafar da Hukumar Kwastam ta yi gwanjo a kan N10,000 kowane karamin buhu a Jihar Legas.
Wasu da dama kuma sun jikkata a turereniyar da ta barke a lokacin da wasu bata-gari suka yi yunkurin shiga ofishin hukumar da ke gwajon shinkafar da karfin tuwo.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da hukumar ta fara gwanjon shinkafar a ofisinta da ke yankin Yaba.
Gwanjon shinkafar da hukumar ke yi wani bangare na yunkurinta rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa da ake fama da ita fadin kasar.
Wata ganau mai suna Comfort James ta ce jami’an kwastam “sun yi bakin kokarinsu wajen shawo kan lamarin amma abin ya gagara, kuma ba a tsara abin sosai ba.
“Dun da cewa ’yan sanda sun zo amma ba su wani taimaka ba, shinkafarsu su ma suka zo karba.”
Amma a martaninsa game da lamarin, kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Maiwada, ya ce, “ba zan iya cewa an samu asarar rai ba, amma akwai wadanda suka sume kuma an kai su asibiti.
“An fara abin cikin lumana a gaban shugaban hukumar kwastam na kasa, har zuwa misalin karfe 5 na yamma.
“Jami’anmu sun kula da jama’a sosai, har zuwa lokacin da aka samu turureniyar daga baya.”
Amma wani likita, Adunola Yemoka, ya wallafa a shafinsa na X cewa daya daga cikin mutanen da aka kai asibiti ya rasu daga bisani.
Hakazalika jami’yyar APC reshen Jihar Legas ta sanar cewa wata daga cikin mambobinsu mai suna Misis Adebanjo Comfort Funmilayo na daga cikin wadanda suka rasu a sakamakon turureniyar sayen shinkafar.