Mutum 71 ne suka mutu a hatsarin motoci a Gombe —FRSC

An yi alƙawarin ƙarfafa dokokin hanya tare da wayar da kan jama’a da kuma haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki don rage aukuwar haɗurra a faɗin jihar.

Mutum 71 ne suka mutu a hatsarin motoci a Gombe —FRSC

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), Reshen Jihar Gombe ta bayyana cewa, kimanin mutane 71 ne suka rasa rayukansu a haɗurran motoci 201 da suka faru daga watan Janairu zuwa Satumba a bana.

Wannan bayanin ya fito ne daga Kwamandan Hukumar FRSC na jihar, Samson Kaura, yayin da yake jagorantar ƙaddamar da yaƙin watannin ƙarshe na shekara, wanda aka fi samun haɗurra a cikinsu na 2024.

Taken yaƙin wannan shekara shi ne: “Yi Magana Kan Tuƙin da ke Barazana: Haɗurra Na Kashe Fasinjoji Fiye da Direbobi,” wanda yake da nufin ba wa fasinjoji ƙwarin guiwa don su san haƙƙinsu kuma su tsaya tsayin daka wajen kare lafiyarsu a kan hanya.

Kaura ya jaddada cewa fasinjoji na da haƙƙin yin tafiye-tafiye lafiya, tare da kira gare su da su riƙa kai rahoton duk wani tuƙin ganganci da direbobi ke yi.

Waɗannan haɗurran da aka ruwaito sun shafi mutane 1,272 da motoci 278, inda mutane 698 suka samu raunuka, wasu 504 suka tsira ba tare da sun sami rauni ba.

Kwamandan ya kuma nuna cewa samu raguwar kashi 9.9% na yawan aukuwar haɗurra idan aka kwatanta da shekarar 2023, haka kuma an samu raguwar kashi 22.2% na mutuwa, kashi 5.5% na raunuka da kuma kashi 11.7% na yawan motoci da suka yi hatsari.

Kaura ya danganta mafi yawan haɗurran da gudun wuce ƙima da ɗaukar kaya fiye da ƙima da tuƙin ganganci da kuma shaye-shaye.

Ya yi alƙawarin ƙarfafa dokokin hanya tare da wayar da kan jama’a da kuma haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki don rage aukuwar haɗurra a faɗin jihar.

“Haƙƙin fasinjoji ne su tabbatar da cewa suna samun tafiye-tafiye cikin tsaro da kariya daga duk wata barazana,” in ji Kaura.

Ya yi kira ga fasinjoji da su guji duk wani abu da zai dauke musu hankali, su rika amfani da belin gaban mota, kuma su kasance masu lura da duk wani tukin ganganci, musamman a wannan lokacin na watannin Ember.

Ya jaddada cewa fasinjoji su ne mafiya shan wahala a hadurra, don haka akwai bukatar su “yi magana kan tukin da ke barazana don kare rayuka a kan hanya.”