Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

Ruwan sama haxe da iska mai karfin gaske sun yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu yayin da mutane da daman gaske suka jikkata.

Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tafiya a saman tirela: Ganganci ko neman sauki?

 

Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

Daga Sani Saleh Chinade Damaturu

Ruwan sama haxe da iska mai karfin gaske sun yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu yayin da mutane da daman gaske suka jikkata. Haka kuma dukiya mai tarin yawa ta salwanta a cikin garin Gashuwa, Hedikwatar Karamar Hukumar Bade ta Jihar Yobe.

Kamar wata majiyar da ke garin na Gashuwa ke tabbatar wa Aminiya cewa, ruwan sama mai haxe da guguwa mai karfin gaske da aka xauki kimanin mintuna 15 ana yi a ranar Laraba da yamma ya lalata gidaje da shaguna da wuraren kasuwanci da kayayyakin sadarwa da sauran gidajen jama’a, lamarin da ya sa mazauna garin da dama suka rasa matsuguni tare da haddasa asarar kadarori da aka kiyasta sun kai miliyoyin naira.

Shugaban Karamar Hukumar Bade, Ibrahim Babagana, ya bayyana wannan iftila’in da faru lamari daga Allah SWT, yana mai cewa, ya haifar da varna mai yawa a cikin al’ummomi da dama a cikin yankin majalisar qaramar hukumar.

A cewarsa, rufin gidaje sun dage, shaguna da dama sun ruguje, kuma iyalai da yawa da masu kasuwanci sun rasa kadarori masu muhimmanci da hanyoyin rayuwa.

Ya ce, “girman varnar ya wuce karfin al’ummomin da abin ya shafa daga karamar hukuma, wadda akwai bukatar gaggawa na gwamnatin jiha ta sa baki don samar da kayan agaji da matsuguni na wucin gadi ga wadanda abin ya shafa,” in ji shi.

Wani mazaunin garin Gashuwa Mustapha Mai kayan miya , ya ce, ruwan saman da kansa bai yi yawa ba, amma guguwar iska da ke tare da shi ce ta haifar da lalacewar da ba a taxa gani ba.

Ya ce, gidaje da dama sun ruguje, yayin da kayayyakin sadarwa suka yi mummunan vaci kuma ta lalata wasu layukan sadarwa da gidaje.

Ya danganta faruwar hakan da karfin guguwar wadda ya ce, yawaitar sare itatuwa a yankin da ke da kusanci da hamadar sahara ya haifar.

Ya bayyana cewa, bishiyoyi a da suna zama wuraren da iska ke busawa, suna taimakawa wajen rage saurin iska da kuma daidaita yanayin qasa na yankin amma yawaitar sare su su ta hanyar noma, share filaye, fadada birane da sarewa don samar da makamashin itacen girki ya sa al’ummomi suka fi fuskantar iska mai tsananin gaske.

Mazauna da dama sun bayyana lamarin a matsayin daya daga cikin mafi munin bala’o’i da suka afkawa garin Gashuwa a cikin ‘yan shekarun nan, suna cewa, magidanta da yawa sun rasa gidajensu da wuraren kasuwancinsu da kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.

Da yake tabbatar da adadin wadanda suka mutu a hukumance, Daraktan Lafiya na Babban Asibiti na Musamman na Gashuwa, Dakta Akinola Adekunle, ya ce, mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.

Ya kara da cewa, dukkan wadanda suka jikkata sun sami magani kuma an sallame su daga asibiti.

A halin yanzu, hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta nuna damuwa game da ruwan sama mai karfi da guguwar iska da ta shafi al’ummomi a Kananan hukumomin Bade da Yunusari da Bursari.

Hukumar ta ce, ta tura Kungiyoyin ba da agajin gaggawa da ma’aikata da masu sa kai daga qananan hukumomin Jakusko da Karasuwa da Geidam da Nguru ke tallafawa, don gudanar da bincike cikin sauri kan al’ummomin da abin ya shafa.

A cewar SEMA, binciken farko ya nuna cewa, daruruwan gidaje sun lalace, inda gidaje masu karamin karfi suka fi yawa a cikin wadanda abin ya shafa.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro